Dan wake da Miya da yaji😋

Teema's Kitchen
Teema's Kitchen @Teema08
Kano State Nigeria

Wayyoo dadi, inacin Dan wakennan kamar karya qara hk naitaji😋😋

Dan wake da Miya da yaji😋

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

Wayyoo dadi, inacin Dan wakennan kamar karya qara hk naitaji😋😋

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

30mint
1 people
  1. 2 cupsFlour
  2. 1 tablespoonGarin kuka
  3. Ruwan kanwa
  4. Dakakken yaji
  5. Albasa 1
  6. attaruhu
  7. Manja
  8. Maggi
  9. Tomatur 5

Umarnin dafa abinci

30mint
  1. 1

    Da farko Zaki zuba flour dinki a roba saiki kawo garin kuka ki zuba, ki jujjuya saiki kawo ruwan kanwa ki kwaba flour dashi

  2. 2

    Ki dora ruwa a tukunya idan ya tafasa ki ringa dibar wannan kwabin flour kina sakawa a cikin ruwan idan kin gama saiki rufe tukunyar ki barshi ya dawo,

  3. 3

    Amma karyi nisa sbd idan ya tafaso ruwan zai xube, kinayi kina juyawa, ko kidan budi murfin tukunyar kadan

  4. 4

    Ki tsame Danwakenki daga tukunya ki zuba a cikin wannan ruwan na roba,

  5. 5

    Saiki ajiye a gefe, shikenan Dan wake ya kammala

  6. 6

    Bayan kamar minti 10 zuwa 15 danwaken ki ya dahu, saeki kawo ruwa a ruba,

  7. 7

    Saiki kawo yankakkiyar albasarki itama ki zuba ki juya, ki kawo Maggi da spices ki zuba ki jujjuya, ki barshi yadan soyu saiki sauke

  8. 8

    Kisa yaji da tumatir da albasan ki Wanda kika yanka,😋😋

  9. 9

    Saiki dauko kasko ki zuba manja, kisa albasa, bayan ya soyu saiki kawo attaruhunki Wanda kika jajjaga ki zuba akan manjan,

  10. 10

    Saiki dauko plate ki zuba danwaken ki, ka kawo wannan miyar da kika soya ki zuba a gefe,

  11. 11

    Ki juya kici da Bismillah😋😋
    Wayyooo dadiii😋😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Teema's Kitchen
rannar
Kano State Nigeria
I love cooking 😍
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes