Dan wake

Ummu HIBBAAN🍝🍓🍉🍇🍌🍜
Ummu HIBBAAN🍝🍓🍉🍇🍌🍜 @fatumar6855
Zaria City, I'm Married💞💞💞

Dan wake abincin gargajiya ne , iyalina suna son girkin gargajiya, don haka sunji dadinsa sosai💃💃💃😋😋

Dan wake

Dan wake abincin gargajiya ne , iyalina suna son girkin gargajiya, don haka sunji dadinsa sosai💃💃💃😋😋

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti talatin
mutum hudu
  1. 1 cupFlour
  2. 4 cupsGarin dan wake
  3. Kanwa
  4. Kuka cokali 3
  5. Dakakken yaji
  6. Tumatir masu karfi
  7. Albasa
  8. Maggi
  9. Mai

Umarnin dafa abinci

minti talatin
  1. 1

    Zaki jika kanwa a ruwa rabin kofi, sai ki tankade garin Dan wakenki da flour da kuka, sai ki juyashi ki zuba ruwan kanwa kadan, Karki cika don kar yayi baki dai dai, sai ki ziba ruwa ba na kanwa ba,ki kwaba Karki cika ruwa.

  2. 2

    Sai ki daura tukunya a wuta ki barshi ya tausa,sai ki fara saka Dan wakenki, ko da cokali ko da hannu

  3. 3

    Ki barshi ya taso amma Karki rufe muffin duka kidan sakayashi don kar ya zube, ya kashe wutan, sai kidan rika juyawa da matsami

  4. 4

    Idan ya tausa sai ki Ciro daya ki matsa cikinsa kigani ko ya dahu,sai ki zuba ruwa a kwano ko roba ki kwasheshi a ciki tas, sai ki fara serving, sai ki kawo yankakkun tumatir da albasa,da da kakken yaji, da soyayyen mai ki ziba💃💃💃💃💃wannan danwaken yayi taushi ga santsi yana wucewa a baki Masha Allah😋😋😋😋😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ummu HIBBAAN🍝🍓🍉🍇🍌🍜
rannar
Zaria City, I'm Married💞💞💞
kullum inason koyan abin da ban iya ba, kuma ina son gwadawa🍕🍤🍗🍜🍡🍝
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes