Dan-wake

Hauwa Rilwan
Hauwa Rilwan @hauwaskitchen
Sokoto

#dan-wakecontest Ina matukar son danwake a rayuwata kuma se Allah ya hadani da miji mai son danwake shi yasa kullum burina in samu sabuwar hanyar da zan sarrafashi😍

Dan-wake

#dan-wakecontest Ina matukar son danwake a rayuwata kuma se Allah ya hadani da miji mai son danwake shi yasa kullum burina in samu sabuwar hanyar da zan sarrafashi😍

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 1&1/2kofi filawa
  2. 1/2kofi garin rogo
  3. 2kofi ruwan kanwa
  4. garin kuka 1 cokali
  5. Gishiri
  6. Maggi
  7. Yajintafarnuwa
  8. Man kuli
  9. Tumatir
  10. Ganyen latas
  11. Kwai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ga kayan hadin danwake.ki jiqa kanwa ki tankade filawa da garin rogo gishiri da kuka cokali daya

  2. 2

    Ki cakud'a filawa da garin rogo da gishiri da garin kuka ki cakud'a komai ya game

  3. 3

    Ki zuba ruwan kanwa a cikin hadin ki kwaba kar yayi tauri yayi laushi yadda ba zeyi qarfi ba

  4. 4

    Ga hadin nan beyi gudaji ba yayi daidai kuma be cika ruwa ba

  5. 5

    Dama a can dayan gefen ke dora tukunya da ruwa akan wuta kin rufe har su tafasa

  6. 6

    Idan ruwanki ya tafasa se ki kama debo kullun danwake kina zubawa iya girmanda kike so ki rufe tukunya ki barshi ya cigaba da tafasa har ya dahu

  7. 7

    In kikaga ya dahu se ki dauko wani mazubi ki zuba ruwan sanyi se ki saka guda daya in kika ga ya taso sama to ya dahu ki kwashe duka in kuma ya sauka qasa to be dahu ba ki bari ya qara dahuwa

  8. 8

    Se ki zuba soyayyen mai a cikin danwake ki zuba a plate kiyi garnishing ni a nawa na yanka tumatir da kwai nasa ganyen latas da kuma yaji

  9. 9
Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Hauwa Rilwan
Hauwa Rilwan @hauwaskitchen
rannar
Sokoto
I love cooking though I'm not perfect but trying to be
Kara karantawa

sharhai

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
@hauwa001 bahaushe yache amarya baki laihi yau mezaa girka mana 😅

Similar Recipes