Tura

Kayan aiki

awa daya
mutum biyu
  1. Semolina Kofi biyu
  2. Gishiri karamar cokali daya
  3. Yeast karamar cokali daya
  4. Ruwan dumi
  5. Albasa matsakaiciya
  6. Atarugu yadda akeso
  7. Maggi da sauran kayan dandano
  8. Dakekken nama

Umarnin dafa abinci

awa daya
  1. 1

    A debi garin semolina Kofi biyu, sai a niqa shi a blender, za aga yayi laushi sosai Kamar flour,a zuba a roba, a nemi yeast karamar cokali daya a zuba.

  2. 2

    A zuba gishiri qaramar cokali daya, a gauraye a debi ruwan dumi a kwaba dashi kamar panke.

  3. 3

    A rufe hadin a barshi a wuri me dumi ya samu kamar minti 30-40. Bayan ya tashi sai a nemo dakakken nama wadda ta sulala, ko Kuma kifi idan ana buqata,sai kayan dandano,atarugu da albasa.

  4. 4

    A yanka albasa kanana, a jajjaga atarugu a fasa Maggi idan ana buqatar wasu kayan dandanon ana iya karawa a ciki. Sai a juye a cikin kwabin semolinar a gaurayesu sosai da sosai su hade.

  5. 5

    Bayan an kwaba dakyau sun hade sai a daura Mai a wuta tayi zafi, a rinqa debar hadin Nan Ana jefawa cikin Mai. A soya ta Kamar panke a wuta Mara karfi sosai.

  6. 6

    Bayan an soya an kwashe ta a mazubi, za a iya cinta da romon mama ko kifi, shayi ko juice ko a cita haka. Tana da Dadi sosai.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
HAFSAT ABDULKAREEM
rannar
A food lover.❤️always ready to learn something new in zha kitchen 🍽️🍩😍
Kara karantawa

sharhai (2)

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
An zuba fasaha a gurin nan masha Allah😋🤝🏼

Similar Recipes