Kayan aiki

1hr
3 yawan abinchi
  1. Gyada danya kofi daya
  2. Danyar shinkafa kofi daya
  3. Danyar citta da kaninfari kadan
  4. Lemon tsami guda 2 manya

Umarnin dafa abinci

1hr
  1. 1

    Da farko zaki gyara gyadar ki ki wanke ta sannan ki jiqa ta kwana,itama shinkafar ki jiqa ta ta kwana,saiki fara gyara gyadar za kiga duk bawon Yana fita saiki cire shi tsaf

  2. 2

    Sannan ki wanke shinkafar ita ma saiki hade su da gyadar kisa citta da kaninfari kadan

  3. 3

    Sai ki markada sannan kisa ruwa sosai ki tace da rariya,saiki zuba a tukunyar ki,ki dora a wuta kiyita juyawa har sai yayi kauri yanda kike so

  4. 4

    Sannan ki yanka lemon tsami ki matse akai kisa sugar da Madara yanda kike so,

  5. 5

    Sannan yana rike ciki saiki dade baki ji yunwa ba

  6. 6

    Zaki iya Sha a haka Zaki iya hadawa da kosai,awara,ko fanke Yana Dadi sosai

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Hygienic Snacks and Spices kn
rannar
I love cooking and making snacks
Kara karantawa

Similar Recipes