Jollof Rice

mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
Kaduna State, Nigeria

#worldjollofday ina son jollof sosai,sirrin jollof ki sa mata isashen kayan miya 👌

Jollof Rice

#worldjollofday ina son jollof sosai,sirrin jollof ki sa mata isashen kayan miya 👌

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa
  2. Kayan miya(tumatir,tattasai,tarugu,shambo da albasa)
  3. Tasty tom tomato
  4. Albasa(sliced)
  5. Mai
  6. Dandano
  7. Gishiri
  8. Garlic &ginger paste
  9. Bay leaves
  10. Spices (nayi amfani da oregano,rosemary da mixed spices
  11. Curry
  12. Minced meat(dafaffe)
  13. Ruwan tafashen nama
  14. Ruwan zafi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki zuba manki a cikin tukunya idan yayi zafi seh ki zuba tasty tom tomato ki barshi ya dan soyu kadan.

  2. 2

    Seh ki zuba albasan da kika yanka ki rage kadan,seh ki saka ginger &garlic paste ki barshi ya kara soyuwa tsamin ya fita sannan seh ki kawo kayan miyanki ki zuba su kara soyuwa tare seh ki zuba kayan kanshinki(spices)da bay leaf,dandano,gishiri da curry ki juya ya kara soyuwa.

  3. 3

    Idan ya soyu seh ki kawo shinkafarki da kika wanke kika tsane ki zuba a ciki ki juya sosai ya hade da kayan miya ki dan soya zuwa yan mintina kadan.

  4. 4

    Seh ki kawo ruwan naman ki zuba a kai ki kara ruwan zafi yanda zeh dafa miki shinkafar seh ki rufe,idan ruwan ya tsotse ya dakko dahuwa seh ki zuba minced meat da sauran albasan idan da bukatar kara ruwa ko dandano seh ki kara ki rage wutan ki rufe tukunyar da foil paper ko buhu sannan ki sa murfin tukunyar ki rufe turirin zeh karasa dafa shinkafar a hankali.

  5. 5

    Idan ya dahu shinkafar tayi laushi seh ci,aci lafiya 😁

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
rannar
Kaduna State, Nigeria

Similar Recipes