Dafadukar shinkafa da soyayyar plantain

Salamatu Labaran
Salamatu Labaran @Salma76
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

1hr
mutum 3 yawan abinchi
  1. 2Shinkafa Kofi
  2. 5Tattasai
  3. 1Albasa guda
  4. 2Plantain
  5. Kayan kamshi
  6. Abin dandano
  7. Nama
  8. Ruwa
  9. Gishiri
  10. Mangyada
  11. Tafarnuwa

Umarnin dafa abinci

1hr
  1. 1

    Da farko a gyara kayan hadi tattasai da albasa da tafarnuwa a wanke a yanka ko jajjage a ajiye a mazbi mai tsafta.

  2. 2

    A wanke nama tsaf a tafasa da albasa da gishiri kadan,a soya.

  3. 3

    Sai a wanke shinkafa a tafasa(Boiling) a sake sa ruwa a tsame a marariki.

  4. 4

    Sai a dauko tukunya a zuba tattasai da albasa da tafarnuwa a zuba a soya kadan sai a kawo kayan kamshi da dandanon a zuba asa nama sannan a zuba ruwa daidai yadda zai dafa shinkafar sai a juye shinkafar aciki a gauraya su hadu asa gishiri kadan in ana bukata.

  5. 5

    Idan ruwan ya tsotse sai a sauketa.
    Zaa iya amfani da man gyda ko manja don yin dafaduka.

  6. 6

    Sai a bare plantain a yanka yadda ake son shape asa gishiri kadan a soya kar a bari ya kone,sai a juye a mazubin abinci ko a raba wa iyali.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Salamatu Labaran
rannar
Am a journalist,love to cook every time.
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes