Dambun Couscous

Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
Kaduna

#nazabiinyigirki duk wanda ya san ni ya san dambu shi ne abinci mafi soyuwa a gareni. Ina son dambu. Shi ya sa har na couscous nake yawan yi saboda yana da sauki sosai. A yau se na yi sha'awar in raba recipe dinshi tare da ku.

Dambun Couscous

Masu dafa abinci 8 suna shirin yin wannan

#nazabiinyigirki duk wanda ya san ni ya san dambu shi ne abinci mafi soyuwa a gareni. Ina son dambu. Shi ya sa har na couscous nake yawan yi saboda yana da sauki sosai. A yau se na yi sha'awar in raba recipe dinshi tare da ku.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

40mintuna
4 yawan abinchi
  1. 1Couscous na kwali
  2. Zogala dafaffa yanda kike son yawanta
  3. 4Attarugu
  4. 1Albasa
  5. 1Tattasai babba
  6. cupGyada soyayya rabin
  7. Dandano yanda zai ji
  8. Curry cokali daya babba
  9. cupMai rabin
  10. cupRuwa kwatan

Umarnin dafa abinci

40mintuna
  1. 1

    Ki samu babban wuri ki juye couscous dinki, sai ki zuba duka kayana hadin da na lissafa a sama.
    Tarugu da albasar jajjaga su za ki yi.

  2. 2

    Ki jujjuya su su hade sannan ki yayyafa ruwa saboda ya yi taushi

  3. 3

    Idan kina da raayi za ki daka gyadar ta zama gari. Amma ni na raba biyu na daka rabi na zuba rabi a yanda take.

  4. 4

    Sai ki samu steamer idan babu kuma colander, ki juye a ciki ki zuba ruwa a cikin tukunya sannan ki dora colander din a kai

  5. 5

    Ki rufe ruf ku bar shi ya turara na tsawon minti talatin ko kuma sadda kika tabbatar ya nuna.

  6. 6

    A ci da ruwa a kusa kar ya shake ku😂

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
rannar
Kaduna
I absolutely love cooking. I can merrily state that my kitchen is my playground in every sense! My mother has always been a wonderful cook, and I feel she is my inspiration.
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes