Fanke

Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
Kaduna

#jumaakadai ina matukar son fanke musamman namu na gargajiya ba irin wanda ake yi ma hade-hade ba. Ina fatan za ki gwada a yau ki sha mamakin dadinshi.

Fanke

Masu dafa abinci 5 suna shirin yin wannan

#jumaakadai ina matukar son fanke musamman namu na gargajiya ba irin wanda ake yi ma hade-hade ba. Ina fatan za ki gwada a yau ki sha mamakin dadinshi.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Awa 1mintuna
3 yawan abinchi
  1. 2 cupsflour
  2. 4tablespoons sugar
  3. 1teaspoon yeast
  4. Pinch of salt

Umarnin dafa abinci

Awa 1mintuna
  1. 1

    Ki zuba flour a babban bowl, sai ki zuba sugar da gishiri ki hade su sosai.

  2. 2

    Ki samu cup dinki ki zuba yeast da warm water (ba mai zafi kwarai ba) sai ki rufe shi ya yi kaman minti biyar idan mai kyau ne za ki ga bubbles sun tashi a sama idan kuma kika ga babu komai ki canja wani yeast din

  3. 3

    Daga nan sai ki kwaba, zai zama ya yi ruwa ruwa saboda ya fi taushi da dadi

  4. 4

    Ki buga shi sosai da iya karfinki ta yanda zai yi taushi kamar irin na kasuwa da kike ci ki rasa wai ma ya suke yin shi? To sirrin shi ne bugun kato😂

  5. 5

    Sai ki rufe ki bar shi a warm place ya tashi kamar minti talatin

  6. 6

    Ki zuba mai a pan, idan ya yi zafi sai ki rinka diba a tsakanin yatsarki babba da mai bi mata shi ne zai sa ya luliye kamar dai yanda nawa ya yi

  7. 7

    Idan ya soyu sai ki kwashe. Za ki iya barbada sugar a kai ko kuma ki bar shi a haka. Ni dai na barbada powdered sugar a nawa

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
rannar
Kaduna
I absolutely love cooking. I can merrily state that my kitchen is my playground in every sense! My mother has always been a wonderful cook, and I feel she is my inspiration.
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes