Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa barjajjiya kofi 2
  2. Tattasai, 5
  3. attarugu, 5
  4. da albasa 2
  5. Sinadarin dandano,
  6. Curry
  7. Mai
  8. Allayahu

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko zaki samu shinkafar ki mai kyau ki Kai ayo maki barzo

  2. 2

    Bayan an kawo sai ki wanke shi kisa a gwagwa kibar shi ya tsane tsaf sai ki Sami madanbancinki ki zuba a ciki ki rufe sai ki Dora kan wuta

  3. 3

    Kisamu tattasai, attarugu, da albasa, ki gyara kiyi grating ko jajjage ya danganta da raayin ki, ki aje a gefe ki daka sinadaran dandano ki aje ki yanka allayahu da wadattar albasa manya manya albasa Kuma slice Dinta zakiyi.

  4. 4

    Sai ki duba dambunki da kika Dora in yayi half done sai ki sauke kisamu roba babba ki zube,

  5. 5

    Ki xuba maggi cikin kayan miya ki hade su (sbd magin yayi saurin narkewa) sai ki zuba akan farin dambun ki ki zuba curry da spices dinki, ki kawo allayahu da albasar ki da kika wanke ko zuba

  6. 6

    Sai kisa kuyahwa ki jujjjuya har sai komi ya hade jikin sa sannan ki zuba mai ki hade.

  7. 7

    Ki Maida a madanbacin ki ki aza bisa wuta ki rufe karkisa wuta da yawa kibashi 20to25minute ya sulala sai ki sauke shikenan kingama dambun ki 😋😋😋

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
humaira Cakes And More
rannar
I love cooking it's my hubby my fashion
Kara karantawa

Similar Recipes