Tura

Kayan aiki

5 yawan abinchi
  1. Shinkafa kofi3
  2. Taliya kwatar leda
  3. Timatir
  4. Albasa
  5. Attaruhu
  6. Tattasai
  7. Mai ludayi 3 da soyayyan nama
  8. Maggi 6 da gishiri kadan
  9. Salad da timatir
  10. Albasa da gurji

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki fara dora ruwan dahuwar shinkafarki idan ya tafasa zaki wanke shinkafa kisa aciki sai kidan juyata kirufe ta dahu, idan takusa nuna zakisa taliyarki sukarasa tare, intayi zaki taceta sai kimaidata wuta ta turara

  2. 2

    Zaki gyara kayan miyarki kiwanke ki jajjaga sai ki dora a wuta zaki dafashi har sai dan ruwan kayan miyar ya kone sai kisa mai ki soya bayan ta soyu sai kisa soyayyan namanki aciki tare da maggi d gishiri kicigaba da soyawa, sai kisa spices akarshe shikenan

  3. 3

    Zaki wanke salad dinki sai ki yankashi kisake wankeshi da gishiri sai kibarshi ya tsane, sannan ki fere gurjinki ki wankeshi sai kiyanka tareda timatir da albasa

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Baby hadejia
Baby hadejia @cook_17645406
rannar
Hadejia

Similar Recipes