Dambun shinkafa 3

Nusaiba Sani
Nusaiba Sani @momtwins02

#OMN inada tsakin shinkafa yayi 1 month ajiye, sai ranar Friday ina tunanin me zanyi na ganshi Amma Banda zogala, finally dai nasamu zogala yau,

Dambun shinkafa 3

#OMN inada tsakin shinkafa yayi 1 month ajiye, sai ranar Friday ina tunanin me zanyi na ganshi Amma Banda zogala, finally dai nasamu zogala yau,

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

2hrs
5 yawan abinchi
  1. 4 cupsBarzajjiyar shinkafa
  2. Zogala me yawa sosai
  3. Man gyada
  4. Curry
  5. Maggi
  6. Lawashi
  7. Sauce

Umarnin dafa abinci

2hrs
  1. 1

    Dama inada barzajjiyar shinkafa Kuma tankadadda jiqawa kawai nayi na tsiyaye ruwan sai na barshi yayi kamar 30 haka a colander.

  2. 2

    Bayan ta tsane, dama na wanke zogala na tsane sai na zuba nasa Maggi fari da curry na motse sosai.

  3. 3

    Sai nasa lawashi kadan saboda inason kamshin shi ya fito.

  4. 4

    Daga Nan sai na wanke tunkunya na zuba ruwa sai na kawo marfi na rufe sannan na zuba hadin dambu

  5. 5

    Bayan kin zuba sai ki rufe ki barshi yayi kamar 30mins haka on medium heat zakiji ya Fara kamshi Kuma idan kin Buda zakiga ya taso sosai sai ki kwashe a wuri me Fadi Kuma me kyau.

  6. 6

    Sai ki zuba sauce dinki ki Dan yayyafa ruwa kadan ki motse kwarai sannan ki maida kan wuta.

  7. 7

    Bayan na maida saina yanka lawashi da albasa na zuba na rufe na barshi ya Kara turara.

  8. 8

    Shikenan dambu yayi sai a sauke a yamutse, kina iya hada coleslaw nidai kwai kawai na yanka naci dashi

  9. 9

    Dambun yayi dadi sosai baa bawa yaro me kiwuya.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Nusaiba Sani
Nusaiba Sani @momtwins02
rannar
I'm a daughter, housewife and a mother. Cooking is my hobby.
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes