Dambun shinkafa

Ayshat Adamawa(U. Maduwa)
Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
Abuja

Hmmm banma san ta inda zan fara bayani ba wallahi Dambu na da dadi wannan shine karona na farkon da naci Dambu kuma tayi dadi sosai yanzu kam na samu sabon girki.. @jaafar and @mrsjikanyari01 wannan naku ne

Dambun shinkafa

Hmmm banma san ta inda zan fara bayani ba wallahi Dambu na da dadi wannan shine karona na farkon da naci Dambu kuma tayi dadi sosai yanzu kam na samu sabon girki.. @jaafar and @mrsjikanyari01 wannan naku ne

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Awa daya da
Biyar
  1. Tsakin shinkafa cupi hudu
  2. Zogale mai yawa
  3. Dakakken gyada
  4. Attarugu guda biyar
  5. Shombo guda biyar
  6. Albasa manya guda uku
  7. Maggi iya yadda akeson
  8. Curry kadan
  9. Mai gyada
  10. Yajin hannu

Umarnin dafa abinci

Awa daya da
  1. 1

    Da farko zaki kai shinkafarki engine a nika miki, idan an kawo zaki iya tankadewa ki cire garin jikin

  2. 2

    Sai Ki wanke shinkafar taji ki ajiye a colander kam ki wanke zogalenki zai dan jiku

  3. 3

    Bayan kin wanke zogalen sai ki zuba akan shinkafa ko chakudasu da kyau sai ki zuba a steamer dinki kiyi steaming na wani lokaci kamar 80% na dafuwarshi haka

  4. 4

    A wannan lokacin zaki zuba jajjagen kayan miyarki da albasa,Kayan kamshi da kikeson, maggi, dan mai sai ki juyasu da kyau har sai sun hade jikin su sai ki sake mai dashi cikin steamer dinki kisa ka a wuta ta gama dahuwa

  5. 5

    Inda zaki gane ta dau dahuwa kamshi zata ciki gida har makwaobta. A cikin steamer din zaki yi anfani da buhu mai tsabta ciki zaki zuba hadin shinkafar taki yin hakan zaisa yayi steaming da wuri

  6. 6

    Daga nan saiki sake samo wani albasan ki soya da mai ki ajiye a gefe wadda idan danbun yayi dashi zakici da dan yajin dakan hannu

  7. 7

    Ga danbum mu nan ta sauka. Also zaki iya cin ta da sauce da yayi muku

  8. 8

    Kinga yadda tayi kyau a ido tayi washer washar da ita sun barka

  9. 9

    Wanga danbum ba a bawa yaro mai kiwa

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Ayshat Adamawa(U. Maduwa)
Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
rannar
Abuja
cooking is my dream and also cooking is all about being creative
Kara karantawa

Similar Recipes