Yam ball

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. doya guda daya,
  2. kwai guda biyu,
  3. tarugu guda hudu,
  4. albasa guda daya,
  5. filawa rabin kofi,
  6. garin biredi rabin kofi,
  7. magi guda uku,
  8. man gyada na suya,
  9. gishiri kadan

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki fere doya ki yanka sai ki wanke kisa akan wuta kisa gishiri aciki idan ya nuna ki sauke kisa a kolanda ruwan ya tsane

  2. 2

    Ki wanke tarugu da albasa ki nika,kisa mai apan sai ki soya kayan miya kisa magi aciki sai ki sauke

  3. 3

    Kisa doya akan a roba ki samu muciya kidan daka sama sama kisa kayan miya da kika soya ki haje su sosai, sai ki mul mula kisa mai a pan idan yayi zafi kisa ki dau ko doyan kisa a filawa sai kwai sannan garin biredi sai kisa a man gyada ki soya

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Amina Aminu
Amina Aminu @cook_13830126
rannar
zaria,kaduna state

sharhai

Similar Recipes