#Dan-wakecontest

Ashmal kitchen
Ashmal kitchen @Ashmal_catering
Katsina

#Dan-wakecontest
A matsayina na Daya daga cikin matan Arewa,ina matukar San Danwake sakamakon abincin mune na gargajiya Kuma abincine dake biyan bukata cikin Dan lokaci.Kuma Ina matukar son in tarbi bakona dashi saboda Yana da matukar farin jini ga al'ummarmu mu na wannan zamanin,dayawansu suna San dukkan nau'in abincinda za'a sa Masa Mai da yaji
Musamman Yan uwana Mata na Arewacin Nigeria.kuma wannnan Danwaken ya kasu Kashi uku zuwa hudu,Filawar Alkama,da rogo da wake ,Sai Danwaken Alkama,Sai Kuma Dan waken Rogo da Filawa
Amma Ni zanyi Danwaken Rogo da Filawa

#Dan-wakecontest

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan

#Dan-wakecontest
A matsayina na Daya daga cikin matan Arewa,ina matukar San Danwake sakamakon abincin mune na gargajiya Kuma abincine dake biyan bukata cikin Dan lokaci.Kuma Ina matukar son in tarbi bakona dashi saboda Yana da matukar farin jini ga al'ummarmu mu na wannan zamanin,dayawansu suna San dukkan nau'in abincinda za'a sa Masa Mai da yaji
Musamman Yan uwana Mata na Arewacin Nigeria.kuma wannnan Danwaken ya kasu Kashi uku zuwa hudu,Filawar Alkama,da rogo da wake ,Sai Danwaken Alkama,Sai Kuma Dan waken Rogo da Filawa
Amma Ni zanyi Danwaken Rogo da Filawa

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Minti Arba'in da biyar
Mutun biyar
  1. Filawa Gwangwani biyu
  2. Garin Danwake(Rogo) gwangani uku
  3. Kuka cokali shida
  4. Kanwa cokali biyu
  5. Ruwa kofi biyu
  6. Kabeji karamin kwallo
  7. Kwai uku
  8. Kokumba DayaTumatir biyu
  9. Albasa Daya
  10. Man gyada(kuli)
  11. Maggi Hudu

Umarnin dafa abinci

Minti Arba'in da biyar
  1. 1

    Bayan uwargida ta tanadi dukkan wadannan kayan aikin zata dauko filawarta da garin Dan waken ta Sai ta tankade su wuri Daya cikin robarta tsaftatacciya daga Nan ne zata dauko kukarta Sai ta zuba a wannan garin Danwake data tankade Sai ta dauko jikakkar kanwarta bayan ta jiku ta taceta saboda kanwa ansameta daga kasa wani lokaci inta kwanta zata tarar kasace daga kasanta Sai a taceta da rariya ko wani mataci Mai kyau.

  2. 2

    Bayan Nan Sai ki dauko ruwanki ki zuba cikin wannnan garin Danwaken ki vigaba da kwabawa kamar Zaki kwabin fanke bayan ya kwabu dama ruwanki na saman tukunya ya tafasa saiki dau wannnan kwababben gari da Kika kwaba.

  3. 3

    Ki Sami cokalinki Mai kyau da Dan ruwa cikin wani wuri kina tsoma cokalinki kina debowa kina kefawa kamar kina jifar kosai ko hannu domin mahaifanmu Allah ya saka masu da alheri mun riskesu sunayin jifar Danwake da hannu Amma hakanma ba illa bane.

  4. 4

    Bayan kin Gama jefawa a cikin ruwa to anan Zaki dan jira na Dan wani lokaci kinayi kina motsa abinki gudun kada ya hade ko Kuma ya taso ya kashemaki wuta,saboda shi da Yana da tasowa to Amma in uwar gida tana kusa tanayi tana juyashi Yana tafasa.Tafasa biyu zuwa uku ya dahu.

  5. 5

    To anan uwargida zata tanadi ruwa masu sanyi cikin tsaftataccen wuri ta kwaso Dan wakenta da abin tsama ta zuba a wannan ruwa Mai sanyi domin zai bashi damar Ida hadewa kamar yadda akeso.

  6. 6

    Sai ki dauko kabejinki ki yayyankashi kanana kanana Sai ki wankeshi ki Dan barshi ya tsane cikin wani dan kwando,daga nan Kuma Sai ki dauko albasarki da kokumbarki da tumatir dinki dama kin wankesu Sai ki yayyankasu daban daban cikin wasu wurare daban to daga Nan fa Sai uwar gida ta tanadi filat dinta Mai kyau ta Debora danwakenan ta zuzzuba sai ta dauko manta da yajinta ta zuba Mai tsakiya yaji koma gefe Daya Don kowa da Yana cin yajinshi Sai ta barbada magi.

  7. 7

    Sai ta dauko kabejinta ta zuba gefe dayana cikin Danwaken gefe Daya tasa kokumba ansamo a wurin yankan ko wane taimai decoration yadda zai burgers Mai Ci ga Ido kamar kwai da it's kokumba Sai to dauko albasarta da tumatir dinki ki zuba a gefe daya ki yayyanka kwanki ki yayyankashi.To fa Uwargida aiki ya kammala.

  8. 8

    Ina Mai tabbatar making uwargida wannan Danwaken bazakiba yaro Mai kiwuya ba,ko maigidan dake zaman majalisa baya dawowar gida da wuri in yacishi Dole ya dawo da zmaan gida.Wannan shine takaitaccen bayani akan # Dan-wakecontest.

  9. 9

    Aci lafiya

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ashmal kitchen
Ashmal kitchen @Ashmal_catering
rannar
Katsina

sharhai

Similar Recipes