Zobo

Shi zobo Wani ganye ne d ake lemo dashi yana da matukar Dadi sannan Yana da amfani sosai ga lafiyar jikinmu Yana taimakawa hanta sannan Yana taimakawa wajen saurin narkar d abinchi sannan Yana sanya nishadi musamman in ka shashi d sanyi #zoborecipecontest
Zobo
Shi zobo Wani ganye ne d ake lemo dashi yana da matukar Dadi sannan Yana da amfani sosai ga lafiyar jikinmu Yana taimakawa hanta sannan Yana taimakawa wajen saurin narkar d abinchi sannan Yana sanya nishadi musamman in ka shashi d sanyi #zoborecipecontest
Umarnin dafa abinci
- 1
DA farko ga abinda muke bukata zobo,citta, kokumba, kaninfari,siga
- 2
Sai ki wanke zobon ki ki zuba a tukunya ki kankare cittar ki ki goga itama kokumbar ki goga Sai ki xuba a ciki wannan zobon naki
- 3
Sai ki xuba kaninfarin ki a tirmin karfe ki Dan daddaka Sama sama
- 4
Sai ki xuba Akan wannan zobon naki ki kawo ruwanki ki xuba
- 5
Sai ki kunna wuta ki barshi y tafasa Sai kisa rariya ki tace Sai ki ajeye Shi a gefe Domin y dan sha iska
- 6
Bayan y wuce Sai ki xuba siga ki juya
- 7
Sai kisa a fridge yyi sanyi ko Kuma kisa kankara a ciki
- 8
Idan Xaki yi adon sugar a Saman kofin ki ga abinda muke bukata siga,lemon tsami,wuka da kuma kofinan ki Sai kisa wuka ki yanka lemon tsamin gida 2 ki cire kwallon Sai ki xagaye Saman kofin d lemon tsamin
- 9
Bayan ki xagaye Saman Sai ki tsoma Saman kofin a cikin sugar ki juya kofin xakiga y makale a Saman Kamar haka
- 10
Sai ki zuba xobon a cikin kofin Sai ki diga zobon kadan a Saman cup din Domin sigan Saman y zama yyi kala 2sai kisa gayen na'a na'a a Saman zobon ki Don ado
- 11
Shikkenan a sha Dadi lpy
Similar Recipes
-
Hadadden zobo😘😘
#zobocontest , Binciken ya nuna cewa ganyen Zobo ya kunshi sinadarin citric acid, Malevich acid da kuma tartaric acid wadanda ke taimakawa wajen Rigakafin Cututtukan suga da hawan jini.Da yake karin haske game da binciken, Dakta Ochuko ya ce yana da muhimmanci a rika shan ruwa Zobo a duk lokacin da aka kammala cin abinci ba tare da sanya masa sikari ba don ganin ba a gurbata sinadiran da ke cikinsa.Ya ce bin wannan tsari na shan Zobo yana taimaka wa wajen rage kiba, sanyi da. Wasu Cututtuka. Sai dai kuma kwararren ya yi gargadin cewa shan Zobo ga mai juna biyu(Ciki) yana da hadari saboda yana iya zubar da jikin .Ya ci gaba da cewa zobon zai iya haifar da zazzabin da jan ido ga mai juna biyu amma ya nuna cewa duk da yake babu wata shaida kan ill ar shan Zobo ga mai shayarwa, ya ba bada shawarar kaurace masa. Umman Amir And Minaal 🎂🍜🍝 -
Zobo mai karas da kokumber
#zobocontest, ana taimaka wa hanta.Yana rage radadin ciwon ciki da mara na mace mai al’ada idan an hada shi da garin citta.Yana kara nauyi (weight).Yana taimaka wa mai hawan jini.Yana hana kumburin jiki ko na cikin jiki.Yana taimakawa wajen narkar da abinci.Farin zobo yana taimaka wa mai tsohon ciki idan ta jika shi tana sha.Masana sun ce zobo musamman bakin nan na temakawa wajen sauko da hawan jini cikin gaggawa saboda ya kan bude hanyoyin jini ne ta yadda jinin zai rinka gudanawa yadda ake bukatar sa. Ana jika zobo ne ka da a saka suga a rinka shan sa kamar ruwa.Wani masani a fannin karatu na alfanun da ke cikin kayan abinci, Dakta Ochuko Erukainure ya bayyana cewa yawaita shan zobo na taimaka wa wajen rage illar hawan jini a jikin dan’adam a sakamakon sinadaran da ke cikinsa. Umman Amir And Minaal 🎂🍜🍝 -
Zobo mai kaninfari da minannas
#zobocontest, kaninfari da minannas sunada matukar amfani a jikin dan Adam, shi yasa nayi amfani dasu.... Umman Amir And Minaal 🎂🍜🍝 -
Zobo
Zobo dai wani ganye ne Wanda ke fito wa a matsayin furen sure/yakuwa, akwai farin shi akwai ja akwai kuma baki, zobo dai Yana da amfani sosai a jikin Dan Adam musammam in ba'a samishi kayan Zaki ba, Ya na maganin hawan jini sannan Yana wankin ciki da dai sauran su #zobocontest HALIMA MU'AZU aka Ummeetah -
Shayin zobo da girfa
Wannan shayin yana wartsakarwa yana sa magidanta nishadi Kuma yana da Dadi yana gyara dandanon bakiYayu's Luscious
-
Zobo na musamman
Zobo na da amfani sosai ajikin Dan adam kuma yana maganin cutittika musamman hawan jini Oum Nihal -
Zobo
Zobo yana da mutukar amfani a jikin dan adam,yana kara lfy da rage chututtuka ajikimmu,ganyan zobo yana kumshe da wasu sunadarai #zobocontest Zhalphart kitchen -
ZOBO DRINK
ZOBO yana da matukar muhinmanci ga lapiar jikin dan adam,ga masu fama da hawan jini yana saukar dashi cikin sauri,yana daya daga cikin sinadarai masu rage teba....Da sauran su. Bint Ahmad -
Lemon cocumber d lemon tsami
A wannan lokacin d muke n xafi wannan Lemo da matukar sanya nishadi musamman in ya dau sanyi mumeena’s kitchen -
-
Zobo
Abin Sha na zobo ana yinshi ne tin iyaye da kakanni a arewacin nijeriya zobo Yana daga cikin abin Sha na hausawa a kasar hausa ana yawan yinsa sosai saboda yana da amfani ana samun zobo a jikin bishiyar yakuwa zobo Yana da amfani a jiki sosai Yana warkar da cutar hawan jini,Yana Kara jini a jiki,Yana taimaka wa wajen markada abinci da wuri aciki Kuma yana da Dadi sosai masana ilimin kimiyya sun gano cewa zobo Yana rage kiba,Yana maganin ciwon hanta, yana Kare jikin Dan Adam daga kamuwa da ciwon cancer(ciwon daji),Yana kariya daga kamuwa da kwayoyin cuta wannan zobon nayi amfani da Kayan ita tuwa masu qara lafiya a jiki kamar kokomba tana Kara karfin ido,lemon Zaki Yana qara sinadari mae gina jiki,na'a na'a da citta suna maganin mura gaba daya dae wannan zobon yana qara lafiya Kuma gashi akwai Dadi sosai idan kuka gwada zakuji dadinshi #zobocontest Fatima Bint Galadima -
Vintage lemonade
#kanostate .yana wartsake mutum kuma yana kara dandanon baki Shiyasa naga ya dace na kawo muku kuma Ku gwada kuma yana da sinadarai masu taimakawa da lafiyar jiki. Duk mutanen da suka sha Sunji dadinshi da fatan zaku gwada. sapeena's cuisine -
-
Zobo
Zobo Yana da amfani ajiki Yana maganin cututtuka da dama a arewacin nijeriya zobo na daya daga cikin abin Sha wanda sukayi fice tin iyaye da kakanni akeyin zobo a arewacin nijeriya zobo Yana da Dadi kwarai da gaske kuma Yana da saukin yi Yana taimakawa Mara lafiya sosai wajen dawo Mae da dandano na bakinsa Yana Kara kuzari a jikin mutum haka zalika yanasa mutum yaji Dadi a ranshi alokacin da yakesha wannan zobon babu kashe kudi Kuma akwae sauri wajen hadawa idan Kun gwada zakuji dadinshi #zobocontest Fatima Bint Galadima -
Zobo
Ana shan sha da sanyi kuma yanada amfani ga lafiyar dan adam musamman hadin da aka mishi zai taimaka sosai a lokacin zafi kamar yanzu. Chef Leemah 🍴 -
Natural Zobo Drink 🥤
Ina son Zobo sosaiShyasa bana gajia d yi SannanNatural Zobo Yana matukar amfani d Kara lfy a jikin dan AdamBa artificial Zobo ba Mum Aaareef’s Kitchen 👩🍳 -
Zobo
Abinsha na zobo ya kasance daya daga cikin abinsha Wanda iyayenmu da kakanninmu suke shaa tun zamanin daa,sannan kuma a binciken magana ilimi sun binciko abinsha na zobo yana kunshe da ma tattarar lafiya da yawa......yana magance ciwuka manta da kana shisa naso na raba wannan abinsha nawa daku domin kuma ku karu kuma Ku infanta lafiyarku......abinsha na zobo yakasance daya daga cikin abinsha danafi Kauna nida mahaifana a dunyar nan barima idan akayi shi a gargajiyance ....sai ka jarraba kakansan na kwarai... Rushaf_tasty_bites -
Zobo
#zobocontest daya daga cikin manyan abubuwan sha masu karin lafiya. Kamar yadda muka sani cewa zobo wani ganye ne wanda ake busarwa, a sarrafa shi domin yin abun sha. A irin wanna lokacin na zafi zobo na da matukar tasiri ga al'ummah. Sau da dama nakan yi shi ga iyalina su sha. Princess Amrah -
Zobo da ganyen lemon grass
Zobo da ganyen lemon grass sunada matukar amfani ajikin Dan Adam #zobocontest Meenat Kitchen -
Zobo mai kayan hadi
A gaskiya ina son zobo musamma indan yaji kayan kamshi ko yayi sanyi sosai gashi yana kara lfy sosai..#zobocontest.Shamsiya sani
-
Zobo mai kayan kanshi beetroot
wannan zobo akwai dadi sosai ga Karin lafiyar ajiki yara suna sonsa sosai. hadiza said lawan -
-
Zobo mai kayan kamshi
Yanda ake yanayin zafin nan abu mai sanyi yana da matukar mahimmanci musamman idan aka ce yana kara lfy zobo yana magani kala kala sanan idan aka hada sa da kayan kamshi mah yana kara lfy sosai yar uwa ki gwada wanan zobon akwai kayan kara lfy a ciki #zobocontest @Rahma Barde -
Kwadan zobo
#CDFWannan kwado yasamo asaline tundaga iyaye da kakanni,girkine memutukar amfani ga jiki kasancewa anyi amfani da zobo,gyada,kowade yasan amfanin zobo ga jikin Dan Adam Doro's delight kitchen -
Zobo drink
Hadin zobo domin watan azumi akwai dadi alokacin buda baki musamman idan da sanyi. #1post1hope Meenat Kitchen -
Gullisuwa Mai nutella
#Alawa a gaskiya tana d matukar dadi sosai in ka sha kamar yar kanti kudai kawai ku gwada yan uwa mumeena’s kitchen -
Zobo
#zobocontest lemon zobo na daya daga ckin natural drinks me kara lafiya a jikin dan Adam,musamman ayishi ta fannin komai yazama natural a ciki .shi lemon zobo a yishi ya turu shine yke kara dadi sanan yana kara dadewa a fridge yanakara turuwa da kara dadi sanan kuma yayin da zaki tace zobonki zaki kara maidashi wuta ya tafasa shima yana saka zobo ya kara tsumuwa .lemon zobo na kara lafiya ta hanya daban daban yana dauke da sinadarin masu amfani sosai a jiki. phateemahxarah -
Zobo mai sanyi
Yanzu da zafi ya fara matsowa zobo yana da amfani a jikin mu saan kuma idan mai sanyi ne zaki jika makoshin da shi ina son zobo gaskia @Rahma Barde -
Lemon cocumber
Hakika wannan lemo yana d matukar dadi sosai sannan yana kara inganta lafiyar jiki hakan yasa bana sanya wajen yinsa sannan kuma baya bukatar abubuwa d yawa cikin minti 15 kingama a I ki I yalaina suna matukar kaunarsa #lemu mumeena’s kitchen -
Zobo
Ina son Zobo saboda amfaninshi ga jikin dan Adam sannan in hadashi ne da kayan lambu da sauran tsirrai don ya bada kamshi mai dadi. Kadan daga cikin amfanin Zobo sune, 1. Yana kunshe da sinadaren Calcium, Iron da fiber wanda suke kara garkuwa ga jikin dan Adam. Sannan akwai acetic acid da tartaric da Vitamin B wanda suke kara lafiya Koda da Zuciya. Sauran abubuwan da nake sawa kuma irin su citta, Kanumfari da cucumber suma duk suna da amfani sosai.#Zobocontest Yar Mama
More Recipes
sharhai (4)