Zobo

Yar Mama
Yar Mama @YarMama
Bauchi

Ina son Zobo saboda amfaninshi ga jikin dan Adam sannan in hadashi ne da kayan lambu da sauran tsirrai don ya bada kamshi mai dadi. Kadan daga cikin amfanin Zobo sune, 1. Yana kunshe da sinadaren Calcium, Iron da fiber wanda suke kara garkuwa ga jikin dan Adam. Sannan akwai acetic acid da tartaric da Vitamin B wanda suke kara lafiya Koda da Zuciya. Sauran abubuwan da nake sawa kuma irin su citta, Kanumfari da cucumber suma duk suna da amfani sosai.#Zobocontest

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

30mintuna
Mutum 6 zuwa 7 yawan abinchi
  1. Zobo Gwangwani 1
  2. 1Cucumber
  3. 2Citta danye
  4. 6Kanumfari guda
  5. Bawon Abarba
  6. Sugar
  7. Ruwan kanwa 1/2 cokalin shayi
  8. Ruwa lita 1.8

Umarnin dafa abinci

30mintuna
  1. 1

    Farko na hada kayan da nake bukata kamar haka

  2. 2

    Sannan na tsince zobo na tas na girgijeshi a ruwa nasa a tukunya na dauraye danyar cittana na daka kadan sai na zuba na wanke bawon abarbana sosai shima na zuba na zuba Kanumfari na masannan na zuba musu ruwa lita 1.8 na tarfa ruwan kanwa 1/2 na karamin cokalin shan shayi komai ya hadu kamar haka

  3. 3

    A zaman jiran Zobo na ya dahu sai na dauko cucumber ta na wanke, na raba gida biyu kashi daya na yankashi a kwance na ajiye a gefe, kashi daya kuma na markada na tace, gasu kamar haka.

  4. 4

    Bayan zobona ya dahu ruwan ya ragu sai na sauke ya dan huce kadan sannan na tace na zuba ruwan cucumber ta a ciki sannan na sa Sugar iya dandanon da nake so.

  5. 5

    Daga karshe na sa a firji yayi sanyi sannan na dauko kofuna na na musu kwalya da sugar na zuba Zobon nasa sauran cucumber ta na dauko alawan yara mai tsinke nayi ado dashi domin ya bada shaawa ga mai sha.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Yar Mama
Yar Mama @YarMama
rannar
Bauchi
Kitchen is my favorite place
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes