Zobo

HALIMA MU'AZU aka Ummeetah
HALIMA MU'AZU aka Ummeetah @cook_12470582
Sokoto

Zobo dai wani ganye ne Wanda ke fito wa a matsayin furen sure/yakuwa, akwai farin shi akwai ja akwai kuma baki, zobo dai Yana da amfani sosai a jikin Dan Adam musammam in ba'a samishi kayan Zaki ba, Ya na maganin hawan jini sannan Yana wankin ciki da dai sauran su #zobocontest

Zobo

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan

Zobo dai wani ganye ne Wanda ke fito wa a matsayin furen sure/yakuwa, akwai farin shi akwai ja akwai kuma baki, zobo dai Yana da amfani sosai a jikin Dan Adam musammam in ba'a samishi kayan Zaki ba, Ya na maganin hawan jini sannan Yana wankin ciki da dai sauran su #zobocontest

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 1Zobo loka
  2. 1Bawon abarban
  3. Babban Kofi 4 na ruwa
  4. cokaliKanumfari rm1/2
  5. 1Citta qarama

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki samu tukunyan ki Mai tsafta ki zuba citta da kanumfari, ki wanke bawon abarban ki zuba, ki dau Raye zobon ki sa, Sai ki zuba ruwa Kofi 3

  2. 2

    Sai ki daura a wuta ki Bari ya tafasa

  3. 3

    Ki Kara Bari ya tafasa sosai Sai ki sauke ki Bari ya huce Sai ki tace, ki zuba ruwa kidan dauraye zobon da kika zuba, a wannan lokacin za ki Iya niqa gurji, da mangwaro da danyen citta ki tace a ciki Shikenan, ko kuma kisa sugar kadan da jolly jus cola da tiara mango, Amma baron shi ba wannan kayan zakin yafi alfanu a jiki.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
HALIMA MU'AZU aka Ummeetah
rannar
Sokoto
A Baker, a mixologist and a foodie, am a huge fan of cooking and I love sharing recipes
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes