Farfesun kayan cikin saniya

Zuwairiyya Zakari Sallau
Zuwairiyya Zakari Sallau @cook_16765791
Kaduna

Shi wannan farfesun kayan cikin yanada matukar dadi,mutane suna sanshi manya da Yara, musamman inya nuna,yana zamawa marasa lfy Abu na farko da zasuci Dan su Sami dandano,wasu suna cin shi haka susha romon,wasu kuma zubawa suke a wata miyan,wasu kuma sucishi da biredi, farfesurecipecontents#

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

minti 45 a tukunya me sauri
3 yawan abinchi
  1. magi me tauraro guda goma da gishiri dan kadan
  2. Attarugu guda takwas
  3. Albasa madaidaita guda biyu
  4. dakakkiyar citta
  5. tafarnuwakayan kamshi da
  6. kayan cikin saniya kilo biyu
  7. Tattasai guda biyu

Umarnin dafa abinci

minti 45 a tukunya me sauri
  1. 1

    Bayan an kawomun kayan ciki,na wankeshi sosai na cire dik wani dattin dake jike

  2. 2

    Bayan na wanke Sena dakko tukunya na zuba a ciki,na yanka albasa akai,nasa magi guda biyar,kayan kamshi da citta,na zuba ruwa bame yawaba na rufe na daura Akan wuta

  3. 3

    Bayan na daura kayan cikina a Kan wuta,Sena dawo gefe na gyara kayan miyana,albasa, tattasai da attarugu nazuba a blender na markada yayi laushi

  4. 4

    Bayan na Gama markadena naxo Wajen tukunyana na bude na zuba markadadden kayan miyan Dana markada,na Kara magina guda biyar da gishiri Dan kadan na juya na rufe

  5. 5

    Bayan kayan cikina ya nuna,na sauke na zubawa kowa nashi,shine kuke ganin hoton nawa,yayi dadi

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan

Wanda aka rubuta daga

Zuwairiyya Zakari Sallau
rannar
Kaduna
cooking is my hobbies
Kara karantawa

Similar Recipes

More Recommended Recipes