Kosan Rogo mai naman kaza

Yar Mama
Yar Mama @YarMama
Bauchi

Mata an sanmu da hikima da yan dabaru musamman a Madafi(kitchen). Koda yaushe idan abu ya saura ina niman hanyar sarrafashi ta yanda zaa ji dadi da shaawan ci. Wannan kosai na yishine da sauran soyayyen naman kaza. #Kosairecipecontest

Kosan Rogo mai naman kaza

Mata an sanmu da hikima da yan dabaru musamman a Madafi(kitchen). Koda yaushe idan abu ya saura ina niman hanyar sarrafashi ta yanda zaa ji dadi da shaawan ci. Wannan kosai na yishine da sauran soyayyen naman kaza. #Kosairecipecontest

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

40mintuna
Hudu
  1. Garin kwaki na tuwo gwangwani biyu
  2. Tattasai guda biyu
  3. Attarugu guda biyu
  4. Albasa rabin babban kwallo
  5. Dunkule guda uku
  6. Man gyada
  7. Sauran soyayyen naman kaza

Umarnin dafa abinci

40mintuna
  1. 1

    Farko de na tanadi kayan da zanyi kosan kamar haka. Na jajjaga kayan miya na sannan na jika namar da ruwan zafi saboda yayi laushi.

  2. 2

    Na tafasa ruwan zafi sai na juye garin a roba mai zurfi na sheka mishi tafashashshen ruwa cikin gwangwani daya na tabbatar ya ratsa koina kamar haka.

  3. 3

    Na barshi ya tsumu na tsawon mintuna uku sai na juye a turmi na kirba shi sosai tare da dunkule da kayan biya amma sai da na gama sannan na yanka mishi albasa. Kafin nan kuma nama ya jika shima sai na bubbugashi sosai a turmi. Gasu kamar haka

  4. 4

    Na wanke turmi na kal sai na juye a ciki na kirba shi tare da dunkule da kuma kayan miya bayan na gama ne na yanka albasa akai sannan naman shima na bugashi sosai a turmi. Gasu kamar haka.

  5. 5

    Na barshi kamar mintina uku sai na wanke turmi na zuba a ciki na kirba tare da kayan yanji da dunkule. Sannan na yanka albasa a kai. Shima naman na buga shi a turmi, gasu kamar haka.

  6. 6

    Sai na juya shi sosai ya hada jikinshi sai na fara marashi da hanuna bayan na sake tsaftace hanuna sai ina sa naman a tsakiyan sai in rufe. Ga yanda nayi.

  7. 7

    Daga nan kuma sai na juya shi sosai ya hade da jikinshi sai na wanke hanuna fes na zo ina mara shi sai in zuba naman a tsakiya sai in hade su, da haka da haka har na gama. Gasu kamar haka.

  8. 8

    Sai na tsabtace hanuna sosai na riga fadadashi da hanu inasa naman a tsakiya sai na rufe kamar haka.

  9. 9

    Bayan na gama sai na soyashi a cikin man gyada mai zafi.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Yar Mama
Yar Mama @YarMama
rannar
Bauchi
Kitchen is my favorite place
Kara karantawa

sharhai

Ayshat Adamawa(U. Maduwa)
Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
@YarMama kaga na manya👍 Allah ya nunamin randa gwada abin nan

Similar Recipes