Soyayyar shinkafa da salak Tareda naman kaza

rashida musa
rashida musa @cook_17709885

#SSMK yarana suna son wannan shinkafar sosai shiyasa nakemusu shi Kwana bibbiyu

Soyayyar shinkafa da salak Tareda naman kaza

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

#SSMK yarana suna son wannan shinkafar sosai shiyasa nakemusu shi Kwana bibbiyu

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa
  2. Albasa
  3. Karas
  4. Kayan dandano
  5. Koren tattase
  6. Attarugu
  7. Salak
  8. Bama
  9. Naman kaza soyayye
  10. Kurkur
  11. Mai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko nadaura shinkafata Akan wuta nasa gishri kadan da kurkur narufeta yatafasa sai nasauke nawanke na ajiye agefe sai nayanyanka su albasata da Karas tareda koren tattase na ajiye agefe sai nadaura tukunya a wuta nasa mai dayayi zafi sai nazuba albasa nadan soyata sai nazuba karas da kayan dandano da kurkur tareda curry da thyme najujjuya sai nazuba ruwa kadan sannan nazuba shinkafa najujjuya sai nasa koren tattase narufeta har yanuna sai nasauke

  2. 2

    Hadin kazata Kuma......dafarko nagyara kazata nawanke natafasata da kayan Kanshi sai nasoyata na ajiye agefe sai nadaura tukunya a wuta nasa mai kadan sai nasa albasa nadan soyata sama sama sai nazuba jajjagen tumatur attarugu da tafarnuwa najujjuya sai nasa kayan dandano najujjuya sai nazuba naman kazan nasake jujjuyawa sai narufeta narage wutan nabarshi zuwa minti goma sai nasauke

  3. 3

    Hadin salak......nawanke salak dina da gishiri sai nayanyankata sannan nazuba a nazubi mai kyau sai nazuba karas dina Wanda na gurza nayanka koren tattase kanana nazuba akai sai nayanka dafaffen kwai kanana nazuba akai da kokumba najujjuya sai nasa bama nacakudasu shikenan aci dadi lfy

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
rashida musa
rashida musa @cook_17709885
rannar

sharhai

Similar Recipes