Chicken soup da Chinese rice

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Wannan abincin yanada dadi sosai kuma bashida wahalanyi

Chicken soup da Chinese rice

Masu dafa abinci 5 suna shirin yin wannan

Wannan abincin yanada dadi sosai kuma bashida wahalanyi

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa
  2. Koren tattase
  3. Karas
  4. Mai
  5. Peace
  6. Gishiri dan kadan
  7. Maggi knoor na chicken
  8. Attarugu
  9. Kwai guda hudu
  10. Kayan hadi na miya kuma
  11. Karas
  12. Dankalin turawa
  13. Albasa
  14. Corn flour chokali daya
  15. Tafasasshen naman kaza
  16. Koren tattase
  17. Attarugu
  18. Mai
  19. Maggi da sauran sinadaran dandano
  20. Curry da thyme
  21. Tafarnuwa
  22. Citta

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki daura shinkafa a wuta idan yatafasa sai kisauke ta ki wanke ki tsaneta a colander ki ajiye agefe. Sannan kiyanyanka su karas dinki da albasa da koren tattase suma ki ajiye a gefe sannan ki jajjaga tafarnuwa da citta da attarugu ki ajiye agefe

  2. 2

    Sai kidaura tukunya a wuta kisa mai kadan sannan kizuba koren tattase da karas ki jujjuya sannan kisa ruwa daidai yanda zaidafa miki shinkafar sannan kisa gishiri kadan da maggi knoor biyu sai ki jajjaga attarugu kixuba sannan kisa peace sai kidauko shinkafar kijuye aciki sannan kidan juyashi komai yahade sai kirufe kibarta. Sai kifasa kwai kibkadashi sannan kisoyata sai ki dagargazashi sannan idan shinkafar takusan dahuwa sai kixuba akai ki jujjuya shikenan sai kibarta takarasa dahuwa

  3. 3

    Sai kisauke. Sai kuma hadin miya. Zaki daura tukunya a wuta sannan kisa mai sai kizuba albasa kidan soyata sannan kizuba tafarnuwa da citta ki jujjuya sai kizuba attarugu sannan kisa ruwa kadan sai kizuba tafasasshen kazan sai kisa maggi da sauran sinadaran dandano sannan kisa curry da thyme kijujjuya sai kizuba ruwa dan dai dai yanda kikeson yawar miyar sannan kuzuba karas da Koren tattase da tafasasshen dankali sai kibarta yadan tafasa sannan ki dama corn flour kizuba akai

  4. 4

    Shikenan sai kidan barta zuwa minti daya haka sai kisauke. Shikenan kingama

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes