Soyyayiyar shinkafa me kayan lambu

Mrs Maimuna Liman
Mrs Maimuna Liman @cook_13862343
Suleja

Soyyayiyar shinkafa me kayan lambu

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa
  2. Mai
  3. Attarugu
  4. Albasa
  5. Gishiri
  6. Sinadarin dandano
  7. Kayan kamshi
  8. Karas
  9. Koren wake
  10. Kabeji
  11. Koren tattase
  12. Mayonnaise
  13. Soyayyen naman kaza
  14. Ruwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    A saka ruwa a kan wuta idan ya tafasa sai a wanke shinkafa a zuba a saka gishiri kadan da curry sai a barshi yayi rabin dahuwa sai a tsiyaye ruwan a juye shinkafan a abun tsamewa.

  2. 2

    A jajjaga attarugu da albasa a zuba a tukunya,a saka mai a dan soya kadan sai a rufe a rage wutan a barshi.

  3. 3

    A yanka karasa da koren wake a wanke a zuba a ciki,sai a saka kayan kamshi da sinadarin dandano,idan karasa din sun fara laushi sai a juye shinkafar a gauraya shi sosai sai a rufe a barshi ya turaru sai a sauke.

  4. 4

    (Salad) A yanka kabeji,a gurza karas a kai sai a saka maggi kadan,a zuba mayonnaise akai a gauraya ya hade,shikenan salad ya hadu.

  5. 5

    (Nama) A jajjaga attarugu da albasa a zuba a abun suya,a saka mai kadan a soya sai a saka kayan kamshi da sinadarin dandano a saka ruwa kadan sai a saka soyayyen naman aciki ayi ta gauraya shi har hadin ya kama jikin naman.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Mrs Maimuna Liman
Mrs Maimuna Liman @cook_13862343
rannar
Suleja

sharhai

Similar Recipes