Bulalar malam

Mmn khairullah
Mmn khairullah @cook_18339957
Sokoto

Kwalama ce wacce yara da manya keso da marmari

Bulalar malam

Kwalama ce wacce yara da manya keso da marmari

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Fulawa
  2. Yest
  3. Farin magi
  4. Barkono
  5. Mai
  6. Gishiri
  7. Maggi star

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko zaki tankade fulawarki bayan saboda kifotarda dattin dake cikinta,

  2. 2

    Saiki zubata acikin mazubi Mai Dan fad'i saiki zuba yest akai tareda magi fari da Dan gishiri kad'an kizuba ruwa Amma bada yawa ba,

  3. 3

    Saiki wanke hannunki kimurza fulawar, kimurza sosai saita hade Kuma kitabbar batayi qulallaiba,

  4. 4

    Saiki riqa murzata a hannunki saitayi tsawo saiki laulayata tafito kamar bulala ki nemi wani plate kibarbada garin fulawa saiki riqa dorawa akai,idan kingama saiki ajeta ciki inuwa,

  5. 5

    Bayan wani lokaci saiki duba zakiga ta kumburo saiki daura Mai a wuta idan yayi zafi saiki dauko bulalarki kirikika sawa cikin ruwan man idan yayi ja alamar soyuwa saiki kwashe,

  6. 6

    Daga Nan Sai ki dauko dakken barkononki dakika daka da Maggi Star saiki zuba kiss soyayyen Mai kijuya sai sun had'e shekenan kin kammala bulalar malam,😋

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Mmn khairullah
Mmn khairullah @cook_18339957
rannar
Sokoto
Ina son girki tun Ina karama,girki kansani nishadi🤩
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes