Miyar awara

Afaafy's Kitchen
Afaafy's Kitchen @mohana10
Kano

Dedicated to Maryaama's kitchen❤

Miyar awara

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

Dedicated to Maryaama's kitchen❤

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti 15mintuna
1yawan abinchi
  1. Awara yanka biyar
  2. 1Albasa babba
  3. 5Attaruhu
  4. 1Jelar kifi sukunbiya
  5. 1Koren tattasai
  6. Sinadarin dandano
  7. tafarnuwaMasoro,citta da
  8. Oil

Umarnin dafa abinci

minti 15mintuna
  1. 1

    Wannan sune kayan da ake buqata,na daka citta,masoro da tafarnuwa tare da attaruhu

  2. 2

    Da farko zaki daura kaskon suya kan wuta ki zuba mai,in yayi zafi ki saka awararki ki soyata sama sama,in yayi ki kwashe,sai ki rage man daidai yadda zai isheki yin miyar sai ki juye albasa ki juya ki barshi yayi minti biyu,kina yi kina juyawa,kisa attaruhu

  3. 3

    Kisa sjnadarin dandano ki juya ki barshi yayi minti biyu,sai kisa kifi ki juye awarar a ciki ki juya sosai ya hade jikinshi

  4. 4

    Ki saka koren tattasai ki juya yayi minti daya ki sauke....qamshi na musamman ne zai riqa tashi,za a iya cin miyar ita kadai,ko aci da shinkafa ko dai wani abinda kk so

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Afaafy's Kitchen
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes