Soyayyar awara da miyar kayan lambu

Afaafy's Kitchen
Afaafy's Kitchen @mohana10
Kano

💥💃

Soyayyar awara da miyar kayan lambu

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan

💥💃

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

30 minti
2 yawan abinchi
  1. 1/2kilo awara
  2. 5Attaruhu
  3. 1Albasa
  4. 3karas
  5. 1koren tattasai
  6. 1/4 cokaliGarin yaji😉
  7. Sinadarin dandano
  8. Curry

Umarnin dafa abinci

30 minti
  1. 1

    Da farko za a yayyanka awara yadda ake son fasalinshi ya kasance sai a zuba ruwa a tukunya da sinadarin dandano da gishiri kadan a juye awara ciki a daura kan wuta a tafasa(saboda zai fi ratsashi)

  2. 2

    In ya tafaso na biyu sai a tsaneshi a daura mai kan wuta a soya ba sama sama

  3. 3

    A cikin wata tukunyar za a zuba mai cokali uku sai a saka yankakken albasa a soyashi har ya fara canza kala sai a saka attaruhu a juya a soyashi na minti daya

  4. 4

    Sai a saka sinadarin dandano,curry da garin yaji a juya a juye awara ciki a cakude😋😋

  5. 5

    Sai a saka koren tattasai a kashe wuta,za a iya ci da shinkafa,burabusko,taliya da sauransu💥

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Afaafy's Kitchen
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes