Alala da sos din kayan lambu

Najma
Najma @cook_13752724
Kano
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

awa daya da rab
hudu
  1. Surfaffen wake-kopi uku
  2. Tattase_biyar
  3. Attarugu-hudu
  4. Albasa-biyu
  5. Tafarnuwa-dede bukata
  6. Danyar citta_dede bukata
  7. Manja-ludayi biyu
  8. Dandano-dede bukata
  9. Gishiri-dede bukata
  10. Soyayyen kifi-daya
  11. Koren tattase-babba daya
  12. Broccoli
  13. Daffan kwai-hudu
  14. Farin leda
  15. Kayan kanshi
  16. Ruwa-dede bukata
  17. Mai -kadan

Umarnin dafa abinci

awa daya da rab
  1. 1

    Xaki surfa wakenki kiwankeshi tas Sai kiyanka albasa,tattase da attarugu ki markada ya markadu sosai

  2. 2

    Sai kijuyeshi a roba mai fadi kixuba manja,dandano,kiyanka albasa ki Kara ruwan dumi dai dai Sai ki gaurayashi sosai Sai ki samu farin ledanki kixuba kullun aciki kisaka Rabin dafaffan kwan Sai ki kulle haka xakiyi tayi harki Gama

  3. 3

    Dama kinrigada kindaura tukunya da ruwa yayi xafi seki sassaka alalan kirufe kibarshi ya nuna

  4. 4

    Ki jajjaga tattasenki,attarugu,tafarnuwa,citta ki yanka albasanki,kidaura tukunya akan wuta kisaka mai kadan idan yayi xafi Sai kisa albasanki kidan soyashi na mintuna karkibarshi yayi brwon Sai kixuba jajjagenki ki soyashi sama sama Sai Kisa kayan dandanonki da kanshi ki gauraya Kisa kifinki,koren tattasenki da broccoli ki gaurayashi sosai ki rufe na minti biyu Sai ki sauke.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Najma
Najma @cook_13752724
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes