Hallakakabo

Umm Muhseen's kitchen
Umm Muhseen's kitchen @cook_20400043
Yobe State

Akwai dadi sosai Ina matukar son hallakakabo

Hallakakabo

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

Akwai dadi sosai Ina matukar son hallakakabo

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Gyada
  2. Mai kadan
  3. Sugar

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki tanadi gyadar ki sai ki bareta, saiki tanadi fray pan ki zuba gyadar aciki ki dora akan wuta kisami cokali kina gaurayawa karki barta ta dade akan wutar sbd karta kone idan kikaji tadau zafi saiki sauke ki murjeta d hannunki amfanin yin hakan zai taimaka miki wajen fitar bayan ta cikin sauki saiki samu turminki mai tsafta ki zuba aciki ki daddakata amma ba sosai ba yadda dai bayanta zai fita idan kika ga bayanta y fara fita saiki tanadi tire ki zuba aciki saiki bushe ta

  2. 2

    Bayan kin bushe ta saiki maida ita cikin turmin saiki daka ta amma fa kar yayi laushi sosai zakiyi dakan ne batsa-batsa saiki juye acikin kwano mai tsafta saiki dakko frying pan dinki ki zuba sugar a cikin sa ki dora akan wuta kina gaurayawa da cokali har sai sugar y narke yayi ja sannan sai ki dakko wannn dakakkiyar gyadar taki ki zuba aciki kina zubawa kina gaurayawa har sai sun hade jikin su saiki dakko wannn tiren naki ki zuba mai ajikin shi saiki juye hallakakabonki a ciki

  3. 3

    Ki bazashi da cokalin hannunki saiki barshi yasha iska zaiyi tauri sosai saiki 6a6allashi aci dadi lafiya 😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Umm Muhseen's kitchen
rannar
Yobe State
cooking is my favorite 😋
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes