Spicy cracker

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

#Bornostate Daga farko dai zanmika godiyata ga sadiya jahun sbd a wurinta nasamu wannan recipe din. Mungode sosai nida iyalaina munji dadinsa sosai

Spicy cracker

Masu dafa abinci 5 suna shirin yin wannan

#Bornostate Daga farko dai zanmika godiyata ga sadiya jahun sbd a wurinta nasamu wannan recipe din. Mungode sosai nida iyalaina munji dadinsa sosai

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Flour kofi hudu
  2. Mai rabin kofi
  3. chokaliGishiri rabin
  4. Paprika chokali daya
  5. Black pepper chokali daya
  6. White pepper chokali daya
  7. Garin citta chokali daya
  8. chokaliTumeric rabin
  9. chokaliCinnamon rabin
  10. Yaji chokali daya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ga abubuwan da muke bukata anan

  2. 2

    Sai ki tankade flour kizuba a bowl sannan kidauko wayannan abubuwan duka kijuye akai sai kuma kizuba yaji shima sannan ki jujjuya komai yahade wuri guda

  3. 3

    Sai kidauko mai kizuba aciki kisake motsawa sosai sannan kidauko ruwa kizuba akai sai kikwaba sosai yayi laushi. Amma kar kisa ruwan dayawa

  4. 4

    Gashinan bayan nagama kwabawa sai narufe nabarta na tsawon minti goma

  5. 5

    Bayan minti goma sai kidauko kisake kwabawa sannan kirabata gida biyu sannan ki dauko dayan ki ajiye agefe sai ki murza dayan yayi fadi sosai sannan kidau wuka kiyankata kamar haka

  6. 6

    Sannan kisake yankata kamar haka

  7. 7

    Sai kidauko daya acikin wayanda kika yankannan sai kisa yasanki biyu kamar haka sannan ki matseta kamar haka ki dannan sosai sai yazama haka

  8. 8

    Bayan kinyi haka sai kidauko chokali mai yatsu ki bubbula kamar haka

  9. 9

    Bayan kingama sai kidaura mai a wuta idan yayi zafi sai kisoya shikenan angama. Za ki iya cinsa haka kokuma da lemo mai tsayi ko kisamo mayonnaise kisa black and white pepper aciki ki jujjuya sannan kici dashi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes