Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti 30mintuna
4 yawan abinchi
  1. 1leda taliya
  2. 6attaruhu
  3. 3tumatur
  4. 5karas
  5. 1kofi peas
  6. 3albasa
  7. 1/4madaidaicin kabeji
  8. 10maggi
  9. 4kofi mai(don suyar taliya)
  10. nama
  11. 1/2 cokalikori
  12. ruwa yadda zai isheki

Umarnin dafa abinci

minti 30mintuna
  1. 1

    Ki farke ledar taliya ki karkarya ta zuwa kanana

  2. 2

    A dora mai a kasko a wuta,idan yayi zafi a zuba taliya a fara soyata,da ta fara sauya kala,sai a kwashe ta,a tsane a kwando don mai ya fita daga jikin ta

  3. 3

    A wanke kayan miya da kayan lambu sosai,a yanka wanda ya kamata,wanda za'a jajjaga a jajjaga

  4. 4

    A dora jajjagen kayan miya a wuta idan yayi a zuba mai kadan a soya,sannan a zuba tafashshen nama maggi da kori da ruwa da peas,a rufe tukunyar a barta ta tafasa sosai

  5. 5

    Idan an duba peas ya dahu sai a zuba taliya a juya a rufe,itan ta dahu a zuba yankakken kabeji da karas,a kara minti 2 sai a sauke.

  6. 6

    Aci dadi lfy🤤

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
M's Treat And Confectionery
rannar
Zoo road,Kano,Nigeria
A Food biochemist by profession and a food lover by passion
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes