Burabuskon alkama meh kayan lambu

mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
Kaduna State, Nigeria

Burabuskon alkama na da dadi sosai ga amfani a jiki.

Burabuskon alkama meh kayan lambu

Masu dafa abinci 13 suna shirin yin wannan

Burabuskon alkama na da dadi sosai ga amfani a jiki.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Tsakin alkama wanda aka turara daidai bukata
  2. Karas
  3. Albasa
  4. Mai
  5. Gishiri
  6. Ruwa
  7. Dandano
  8. Koran tattasai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki samu ruwa ki zuba a tukunya dai dai yadda kike son sanwar ki,seh ki rufe ya tafasa.Dama kin yanka karas,albasa da koran tattasai yadda kike so.Idan ruwan ya tausa seh ki zuba dan mai kadan a ciki ki zuba gishiri da dandano.

  2. 2

    Seh ki zuba karas dinki da albasa ki barshi ya tafaso.seh ki zuba koran tattasai ki kawo tsakin ki ki samu muciya kina zubawa kadan kadan kina kadawa har yayi taurin da kike so amma karyayi tauri sosai kuma kar yayi ruwa seh ki rufe da foil paper ki rufe da murfin tukunya ki rage wuta ya turara.

  3. 3

    Idan biskin ki yayi zaki ji yana kanshi kuma idan kin dibi kadan kin dandana zaki ji ya dahu yayi laushi.seh ki sauke ki kwashe.Ana iya ci da taushe,parpesu,dage dage ko duk miyar da kike so aci lafiya.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
rannar
Kaduna State, Nigeria

sharhai

Similar Recipes