Alopuri ll

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Yanada dadi sosai kuma bashida wuyan yi don haka nakeyiwa iyalaina sbd suna sonshi sosai

Alopuri ll

Masu dafa abinci 4 suna shirin yin wannan

Yanada dadi sosai kuma bashida wuyan yi don haka nakeyiwa iyalaina sbd suna sonshi sosai

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Flour kofi uku
  2. Ridi chokali uku
  3. chokaliGishiri rabin
  4. cupSemolina quarter
  5. Dankalin turawa guda uku dafaffe
  6. cupMai quarter
  7. Miya
  8. Nikakken nama
  9. Attarugu
  10. Albasa
  11. Citta
  12. Tafarnuwa
  13. Corn flour
  14. Peas
  15. Koren tattase
  16. Dafaffen dankali guda uku
  17. Maggi
  18. Curry da thyme
  19. Onga classic
  20. Madish

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zakitankade flour kizuba bowl sai kizuba semo da ridi da gishiri kijujjuya sai kisa mai kisake jujjuyawa sannan kidauko abun gurza kubewa sai kigurza dafaffen dankalin naki akai kamar haka sai kijujjuya kizuba ruwa kamar rabin kofi kikwaba

  2. 2

    Bayan kinkwaba sai kirufe kibarta zuwa minti goma sannan kidauko kisake kwabawa sai kirabata kashi goma ko fiyeda haka sannan sai kirika dauko daya bayan daya kina murzawa

  3. 3

    Bayan kingama murzawa sai kidaura mai awuta idan yayi zafi sai kidan rage wutan sannan kidauko daya kisa amai sai kidauko ludayi kirika diba man kina zubawa akai zakiga yakumburo sannan sai kijuya kici gaba da watsa man akai har yasoyu sai kicire kisake saka wani. Haka zakiyi tayi har kigama

  4. 4

    Miya kuma zaki daura tukunya a wuta kisa mai kadan sannan kizuba albasa kidan soyata sama sama sai kidauko nikakken nama kizuba akai sannan kisa citta da tafarnuwa kijujjuya har naman tacanza kala sannan kizuba ruwa kofi daya da rabi sai kisa maggi da sauran kayan dandano sai kizuba attarugu sannan kiyanka dankalin kanana kizuba akai kijujjuya sai kisa peas da koren tattase sannan kibari yadan tafasa sai kidiba corn flour dan kadan sannan kidama da ruwa kikada akai shikenan sai kisauke.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes