Potato omelet

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Yanada dadi sosai wurin yin breakfast da ita kuma babu wuyan yi #girkidayabishiyadaya

Potato omelet

Masu dafa abinci 6 suna shirin yin wannan

Yanada dadi sosai wurin yin breakfast da ita kuma babu wuyan yi #girkidayabishiyadaya

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Dankalin turawa manya guda biyar
  2. Karas yan daidai guda biyu
  3. Koren tattase babba daya
  4. Ganyen albasa
  5. Albasa
  6. Attarugu
  7. 5Kwai
  8. Mai
  9. Peace
  10. Tumeric
  11. Maggi dunkule da knoor
  12. Curry da thyme tareda onga classic
  13. Black pepper
  14. Dasauran sinadaran da kikeso

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ga kayakin da muke bukata anan

  2. 2

    Sai kidauko tukunya kiwanke dankalin kizuba aciki sai kisa ruwa kadan da gishiri kidaura a wuta kibarshi yatafasa kamar minti hudu sannan sai kizuba karas da peace kibarsu sununa amma ba sosaiba idan yanuna sai kisauke kitsane ruwan sai kibarta tahuce

  3. 3

    Idan yawuce sai kizuba a bowl ko wani roba mai fadi sannan ki jajjaga Attarugu kizuba akai sai kisa albasa Koren tattase da ganyen albasa kijujjuya

  4. 4

    Bayan kinxuba komai sai kijujjuya sosai komai tahade gabadaya

  5. 5

    Sannan sai kifasa kwai kizuba sai ki jujjuya. Sannan kidaura nonstick pan a wuta kisa mai kadan idan yayi zafi sai kizuba rabi kidan rage wutan kibarta tasoyu Idan dayan gefen yayi sai kijuya dayan gefen a hankali itama tasoyu

  6. 6

    Idan tayi sai kicire kisake zuba mai kadan sai kizuba ragowar itama kisoyata sai kisauke sannan kiyankata kamar yanda nayi haka shikenan aci dadi lfy

  7. 7
Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes