Farfesun kifi me dankalin turawa da albasa

Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
Kano, Meduguri Road, Tarauni.

Yawancin lokuta Inada komai a ajiye, shine yake bani kwarin gwuiwar sarrafa komai ta inda Naga dama. Cikin ikon Allah Kuma sai na dace dandanon ya fita daban. Emily face☺️ Na yarda girki Yana tafiya ta hanyar kirkirowa hade da amfani da tsirrai, kayan lambu yayan ittauwa d.s.s. Ayi dahuwa cikin Jin dadi😍

Farfesun kifi me dankalin turawa da albasa

Yawancin lokuta Inada komai a ajiye, shine yake bani kwarin gwuiwar sarrafa komai ta inda Naga dama. Cikin ikon Allah Kuma sai na dace dandanon ya fita daban. Emily face☺️ Na yarda girki Yana tafiya ta hanyar kirkirowa hade da amfani da tsirrai, kayan lambu yayan ittauwa d.s.s. Ayi dahuwa cikin Jin dadi😍

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

wadataccen lkc
mutum 2 yawan abinchi
  1. 1Kifi babba guda
  2. Kayan kamshi duk Wanda kike dashi
  3. Tafarnuwadomin bukata
  4. Maggie domin dandano
  5. Mai
  6. Jajjagen tarugu da albasa daidia misali
  7. 5Dankalin turawa kamar guda
  8. Albasa guda 2 a rabata gida 4
  9. Alayyahu domin kwalliya
  10. Lemon tsami
  11. Masoro kadan
  12. Ganyen Bay leef guda 1 babba
  13. Karamin icen cinnamon

Umarnin dafa abinci

wadataccen lkc
  1. 1

    Ga abubuwan da nai amfani da su.

  2. 2

    Zaki fara da wanke kifinki ya fita tas ki Buda cikin ki matsa lemon tsami ki tabbatar ya fita. Sai ki tsane a kwalanda. Na wanke su duka sai na dau Wanda zanyi amfani dashi na Adana sauran a gidna Kankara

  3. 3

    Sannan ki hada kayan kamshi da spices, Maggie masoro, citta, Mai ki hade guri daya

  4. 4

    Sannan ki shafa a jikin kifin koina da Ina kina shafawa kina mats alemon Tsami

  5. 5

    Ki Dora tukunya kan wuta, ki zuba mai sai ki jefe bay leaf, ki zuba rosemary da Itacen cinnamon ki motsa sannan ki zuba yankakkiyar albasa ki motsa

  6. 6

    Sannan ki zuba jajjagen tarugu da albasa

  7. 7

    Sannan ki zuba kayan Miya cokali 1 ki motsa

  8. 8

    Sai ki maida wutar low sosai ki saka sazon

  9. 9

    Garam masala

  10. 10

    Ki barbada dan kadan sbd Kar yayi yaji

  11. 11

    Ehen inasonsa hot hot

  12. 12

    Curry powder

  13. 13

    White pepper

  14. 14

    Grounded cumin

  15. 15

    All spice mix

  16. 16

    Hi jajjaga tafarnuwa Ada masoro ki zuba akai

  17. 17

    Sannan ki tsiada ruwa

  18. 18

    Ki saka magie daidai yanda zaiji

  19. 19

    Dama kin feraye dankali Sia ki zuba a ciki a gudansa ki motsa sai ki rufe ki Dan Kara wuta ya dahu a hankali

  20. 20

    Gashi ya dahu, zakiga ruwna ya Kara kauri idan me Romo sosai kike so Sia ki Kara ruwan zafi😍😋

  21. 21

    Sai kidauko gidan kifin ki sa a tsakiyar hadin ki Kuma rage wuta sosai ya turaru

  22. 22

    Sai ki kawo yankakkiyar albasa ki zuba akai ki rufe mintuna 2 ki sauke.

  23. 23

    Wayyo Dadi ba a magana, ki juye a kwano ki Yi ado da alayyahu♥️🧡💛💚💙💜

  24. 24

    Ranar na mashi tutar sarrafa kifi😍🥰💃💃💃

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
rannar
Kano, Meduguri Road, Tarauni.
cooking is my dream!!!
Kara karantawa

Similar Recipes