Taliya da macaroni me alayyahu da dambun nama

Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
Kano, Meduguri Road, Tarauni.

#Taliya
#0812
#girkidayabishiyadaya
Sai an gwada akan San na kwarai, Amma tayi dadi dandanonta ma na musamman ne.

Taliya da macaroni me alayyahu da dambun nama

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

#Taliya
#0812
#girkidayabishiyadaya
Sai an gwada akan San na kwarai, Amma tayi dadi dandanonta ma na musamman ne.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

25mintuna
8 yawan abinchi
  1. Leda daya da rabi na macaroni
  2. Rabin Leda na taliya
  3. Dambun nama daidai misali
  4. Soyayyen nama yanda ake so
  5. Jajjagen tarugu da albasa yanda zaiji
  6. Kayan dandano
  7. Kayan kamshi
  8. Albasa
  9. Alayyahu
  10. Tafarnuwadomin bukata

Umarnin dafa abinci

25mintuna
  1. 1

    A fara da soya taliya da macaroni a tsane a ajiye a gefe

  2. 2

    Sannan a daura mai akan wuta a yanka albasa Idan yayi zafi sai a zuba jajjage a motsa.

  3. 3

    Sannan a zuba soyayyen nama akai

  4. 4

    A juya a tsaida ruwa da ruwan zafi a saka kayan kamshi

  5. 5

    Sannan a saka curry

  6. 6

    A saka maggie da tafarnuwa sai a rufe a barshi ya tafasa

  7. 7

    Idan ya tafasa sai a dandana aji Idan komai yaji sai a kawo taliya da makaronin a zuba akai a juya a rufe

  8. 8

    A barta ta dahuwa kada a cika wuta, Idan ta kusa dahuwa sai a kawo dambun nama a zuba akai a Dan motsa kadan

  9. 9

    A yayyanka alayyahu da albasa yankan manya a wanke sai a zuba a juya su hade sai a kashe wutar, turirin abincin zai sa alayyahun ya dahu.

  10. 10

    Sai a sauke a zuba a ci da zafinta. Ita makaroni ko takiya cinsu da zafi yafi dadi

  11. 11

    Yum yummy??!!

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
rannar
Kano, Meduguri Road, Tarauni.
cooking is my dream!!!
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes