Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki feraye doya sai ki wanke kisa gishiri kadan sai ki dafa.
- 2
Zaki wanke kifi sai ki yanka albasa da citta da tafarnuwa aciki sai kisa maggi ki dafa.
- 3
Zaki gyara attaruhu da albasa sai ki wanke ki jajjaga su.
- 4
Zaki dakko doya da kifi sai ki dakasu sama sama sai ki hadesu guri daya sai ki dakko attaruhu da albasa ki zuba aciki kisa maggi da curry sai ki juya sosai sai ki dinga diba da hannu kina mulmulawa har ki gama.
- 5
Zaki fasa kwai acikin roba me Kyau sai ki kada kisa gishiri kadan aciki sai ki dakko yam ball dinki kisa acikin ruwan kwai sai ki daura mai akan wuta idan yayi zafi sai ki dakko yam ball dinki daga cikin ruwan kwai sai ki soya a mai haka zakiyita yi har ki gama.
- 6
Ga yam ball dinmu nan yayi sai asha da tea ko lemo.
Cooksnaps
Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!
Similar Recipes
More Recipes
sharhai