Tura

Kayan aiki

  1. 2Fulawa Kofi
  2. Sugar 1/4 kofi
  3. Madara cokali 3
  4. Yis 1/2 cokali karami
  5. Kwai Rabin guda,
  6. Ruwa 2/3 kofi
  7. Butter cokali 1
  8. Vanilla flavour cokali 1 karami

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki sami mazubi,ki saka fulawa,sugar, madara, yis,sai ki gauraya.
    Sai ki fasa kwai rabi ki saka.

  2. 2

    Sai ki zuba ruwa ki kwaba doughnut dinki,ki saka flavor,ki saka butter.

  3. 3

    Sai ki hand mixer kiyi kneading din shi.har yayi laushi sosai.

  4. 4

    Sai ki raba dough din gida 8.
    Sai kiyi kneading din kowanne,kiyi mai shape din ball.

  5. 5

    Sai ki yanka parchment paper,ki daura kowanne akai. Sai ki shafa butter akai.

  6. 6

    Sai ki aje a guri mai dumi y tashi,

  7. 7

    Sai ki zuba mai a pan mai Dan yawa,sai ki daura kan wuta.kada ki bari yayi zafi sosai.
    Ba'a saka wuta da yawa wajan suyarsa.

  8. 8

    Sai ki dauko doughnut dinki har wannan paper, sai ki kifa a cikin mai,sai ki bar shi y soyu.

  9. 9

    Idan dayan gefen y soya sai ki juya dayan,zakiga y yimiki wnn zoben.

  10. 10

    Idan yayi sai ki tsame doughnut dinki.

  11. 11

    Sai ki saka shi a cikin sugar din,ki saka y ji ko'ina.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Fatima muh'd bello
Fatima muh'd bello @bakerstreat
rannar
Sokoto
cooking is my passion
Kara karantawa

Similar Recipes