Suya

Walies Cuisine
Walies Cuisine @ummuwalie
Sokoto

Alhamdulillah na kwana 2 da nayima aunty Jamila alqawarin posting inshi sai yanzu lokaci yayi. Yara suna son shi sosai kuma yana da Dadi sosai. Sakkwatawa ga naku har da kowa ma.

Suya

Alhamdulillah na kwana 2 da nayima aunty Jamila alqawarin posting inshi sai yanzu lokaci yayi. Yara suna son shi sosai kuma yana da Dadi sosai. Sakkwatawa ga naku har da kowa ma.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

30 mintuna
mutane 5 yawan
  1. Kofi 3 na garin rogo
  2. Jajjagen tarugu da albasa
  3. Gishiri
  4. Sinadarin dandano
  5. 2Kwai (egg)
  6. Yaji dakakke
  7. Ruwan dumi
  8. Mai domin suya

Umarnin dafa abinci

30 mintuna
  1. 1

    Ki zuba garin rogo ki hada da gishiri, sinadarin dandano, jajjagen tarugu da albasa ki motse sai ki zuba ruwan dimi kadan baya son ruwa da yawa ki kwaba.

  2. 2

    Sai ki mulmula shi kamar yadda Kika Gani a hoto, sai ki fasa kwai a kwano kisa jajjagen tarugu da albasa kisa gishiri, sinadarin dandano ki motse. Bayan ki mulmula sai ki kadan acikin ruwan kwai sai ki zuba acikin mai me zahi Amma wuta kadan kina juyawa har ya soyu.

  3. 3

    Idan kin kwashe sai ki zuba dakakke yaji ki motse... Aci Dadi lahiya...

  4. 4
  5. 5
  6. 6

    Akwai wata hanya ta sarrafa suya batakai laushin ta farkon ba; bayan kin kwaba ki mulmula sai ki soya sannan kisa acikin hadin ruwan kwai ki sake soyawa.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Walies Cuisine
Walies Cuisine @ummuwalie
rannar
Sokoto
Ummu wali by name, I love creating new recipes and cooking is bae***😍
Kara karantawa

sharhai (37)

Firdausi Musah
Firdausi Musah @Fydeeh44
@ummuwalie mun gde sosae,Allah ya qara baseera,saemun gwada insha Allah

Similar Recipes