Tuwon shinkafa miyar wake

Meenat Kitchen
Meenat Kitchen @meenat2325
Kano State

Miyar wake akwai dadi sosai musamman idan kin hada da tuwo ko biski

Tuwon shinkafa miyar wake

Miyar wake akwai dadi sosai musamman idan kin hada da tuwo ko biski

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

1:20mintuna
5 yawan abinchi
  1. Shinkafar tuwo Kofi biyu
  2. Surfaffen wake Kofi daya
  3. Kayan miya Kofi daya
  4. Sinadarin dandano
  5. Gishiri da curry
  6. Kayan kamshi
  7. Manja da man kuli

Umarnin dafa abinci

1:20mintuna
  1. 1

    Dafarko zaki samu tukunya kisa ruwa ki Dora a wuta idan ta tafasa ki wanke shinkafar ki zuba

  2. 2

    Idan shinkafar ta dahu kisa muciya ki tuketa, saiki bata mintuna 5 daganan saiki kwashe tuwanki ya kammala

  3. 3

    Saiki samo tukunya kisa ruwa idan ya tafasa kisa surfaffen wakenki da kika wanke kika gyara kika cire duk wani hancinsa idan waken yayi taushi saiki saukesa

  4. 4

    Saiki dauko tukunya kisa manja da man kuli kisa kayan miya ki soya idan ya soyu kisa ruwa daidai yanda kikeson miyarki ta kasance a yawa

  5. 5

    Saiki sa sinadarin dandano,gishiri,curry,da kayan kamshi, idan ya tafasa kisa waken amma saikin Dan yi mashing din sa kadan

  6. 6

    Idan niyarki yayi kaurin da kikeso saiki sauke aci da tuwon nan da kika kwashe

  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Meenat Kitchen
Meenat Kitchen @meenat2325
rannar
Kano State
my name is Amina Mohd Sani, cooking is my fev,cooking is my hubby......
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes