Faten dankalin turawa

Hannatu Nura Gwadabe
Hannatu Nura Gwadabe @Umcy1997
Kano

#ramadanclass Nayi shi sbd maigida zaije aiki da wuri km Yana sauri shiyasa na masa shi saboda Yana so km yaji dadin sa. Yana sauri sosai shiyasa hoton baiyi clear ba sbd Yana turiri km na riga nasa a warmer tunda iya cikinsa nayi

Faten dankalin turawa

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

#ramadanclass Nayi shi sbd maigida zaije aiki da wuri km Yana sauri shiyasa na masa shi saboda Yana so km yaji dadin sa. Yana sauri sosai shiyasa hoton baiyi clear ba sbd Yana turiri km na riga nasa a warmer tunda iya cikinsa nayi

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

awa 1mintuna
1 yawan abinchi
  1. 12Dankali kananu guda
  2. Mai
  3. Attaruhu, tumatir da albasa
  4. Karas da koren tattasai
  5. Curry, spices da dandano
  6. Tafarnuwada girfa

Umarnin dafa abinci

awa 1mintuna
  1. 1

    Da farko na tanadi kaya na kmr haka

  2. 2

    Na fara da fere dankali na wanke shi na ajiye ba tare Dana yanka ba tunda kananu ne sai na gyara attaruhu da tumatir nayi blending din su na yanka albasa na goga tafarnuwa sai nasa Mai a tukunya nasa albasa, tafarnuwa da stick na girfa(girfa tana dadi sosai a faten dankali sbd wani qamshi na musamman take sawa) saina yita juyawa da suka soyu na zuba kayan Miya bayan sun soyu na tsaida ruwa na zuba dankali, dandano, curry da spice na rufe don yayi laushi

  3. 3

    Na yanka karas Dina manya da albasa da koren tattasai na zuba karas da albasa na rufe don suyi laushi bayan sunyi laushi na duba dankali Naga ya dahu lugub sosai na Dan farfasa shi nagani sai na zuba koren tattasai na rufe bayan minti biyar na sauke (Ana iya sa kifi ko nama).

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Hannatu Nura Gwadabe
rannar
Kano
Ina matuqar son girki
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes