Tuwon Amala da miyar karkashi me stew

Habiba Abubakar
Habiba Abubakar @UmmuMuhammad2
Sokoto

Abincin mutanen kudu ne #yclass

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti 35mintuna
mutum 1 yawan a
  1. Garin Amala (ko na rogo ko na doya)
  2. Ganyen kalkashi
  3. Kayan miya
  4. Gishiri
  5. Maggi
  6. Man gyada
  7. Nama
  8. Busasshen kifi
  9. Kayan kamshi
  10. Ruwa
  11. Kanwa

Umarnin dafa abinci

minti 35mintuna
  1. 1

    Zaki wanke naman ki tafasa

  2. 2

    Sannan ki gyara kifinki ki dauraye da ruwan zafi

  3. 3

    Sannan ki gyara kayan miyan ki nika

  4. 4

    Sai ki zuba ruwa cikin tukunyar ki ki daura a wuta

  5. 5

    Sannan ki zo ki zuba Mai a wuta in yayi zafi ki sa Yar albasa kadan sannan ki zuba namanki ki soya sama sama

  6. 6

    Sai ki juye nikakken kayan miyanki a cikin man Nan Mai nama sai ki zuba kifin da Kika dauraye sanann ki juya Sai ki rufe

  7. 7

    Sai ki koma wurin ruwan da Kika daura a wuta idan ya tafasa Sai ki rage wutan sannan ki dakko garinki ki dinga zubawa a cikin ruwan kina tukawa da muciya

  8. 8

    Har Sai ya Yi kauri yanda kike sonshi sannan ki gyara bakin tukunyar ki rufe Sai ki barta ta silala Kamar minti 20

  9. 9

    Sai ki rufe ki rage wuta in ya nuna Sai ki sauke sannan ki kwashe amalanki ko cikin leda ko ki mulmula da koko

  10. 10

    Sannan ki koma wurin miyarki ki sa gishiri da Maggi da kayan kamshi

  11. 11

    Sai ki jefa Yar kanwa kadan ki sa Dan gishiri da Maggi sannan kisa maburgi ki burgeshi

  12. 12

    Sannan ki daura wata tukunya a wuta Sai ki zuba ruwa kadan a ciki ki gyara ganyen kalkashinki ki zuba cikin ruwan in ya tafaso

  13. 13

    Shikenan tuwon amalanki ya hadu da Kuma miyar kalkashi Wanda zaa hadashi da stew

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Habiba Abubakar
Habiba Abubakar @UmmuMuhammad2
rannar
Sokoto
cooking is full of fun
Kara karantawa

Similar Recipes