Banga soup

Meenat Kitchen
Meenat Kitchen @meenat2325
Kano State

#wazobia, palm nut soup wadda akafi sani da Banga soup miyar kabilar Niger Delta ne wato bangaren south eastern part na Nigeria wadda kabilar igbo ke kiranta da ofe akwu, miyace Mai tattare d akarin lapia da Karin jini ajikin mutum naji dadinsa sosai shiyasa nayi maku sharing domin ki gwada wa iyalanku.

Banga soup

#wazobia, palm nut soup wadda akafi sani da Banga soup miyar kabilar Niger Delta ne wato bangaren south eastern part na Nigeria wadda kabilar igbo ke kiranta da ofe akwu, miyace Mai tattare d akarin lapia da Karin jini ajikin mutum naji dadinsa sosai shiyasa nayi maku sharing domin ki gwada wa iyalanku.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

awa 2 zuwa 3mintuna
10 yawan abinchi
  1. 1/2mudu na kwakwar manja
  2. Kofi daya na cray fish
  3. Sent leaf (daddoya)
  4. Sinadarin dandano iya bukata
  5. White papper babban cokali daya
  6. Attarugu iya yanda kikeson yajin miyarki ya kasance
  7. Busasshen kifi guda biyu
  8. Ganda iya bukatarki
  9. Naman rago Kona sa Wanda kike dashi akusa
  10. tafarnuwaAlbasa da
  11. Banga spices na dari biyu
  12. Bangaren mahadi kuma
  13. Garin sakwara na kanti

Umarnin dafa abinci

awa 2 zuwa 3mintuna
  1. 1

    Wannan sune kayan amfanina gaba daya kayan banga soup Zaki samesu a sabon gari ga wadanda suke zaune a kano kenan, Zaki samu a sabon gari gurin yarabawan Nan Amma saikin shiga cikin Yan kura sosai Zaki samu

  2. 2

    Dafarko Zaki wanke nama da kwakwar manja dinki Zaki zuba nama a tukunya kisa ruwa da albasa sai Maggi da gishiri ki tafasashi itama kwakwar manja kisata a tukunya daban kisa Ganda da ruwa ki dafata ta dahu

  3. 3

    Idan ta dahu ki sauke ki tace ruwan kisata a turmi ki daketa

  4. 4

    Idan ta daku kisa wannan ruwan da kika tafasata aciki saikisa kwalanda ki tace kisa Dan ruwa kadan ki matse tsaf

  5. 5

    Idan kin matse ki dauki ruwan ki Dora akan wuta yaita dahuwa saiki yanka attarugu da sent leaf wato (daddoya) abunda yasa ba'ayin jajjage saboda ba'ason attarugun yayi ruwa

  6. 6

    Saiki zuba a kan miyarki da ganyen sent leaf din kadan saikisa Banga spices

  7. 7

    Saiki jika busasshen kifi da ruwan zafi da gishiri ki wankesa tas ki dauko gandarki ki yankata kananu ki hadeta da nama saiki zubasu acikin miyar

  8. 8

    Ki dauko gyararren busasshen kudinki shima ki zuba sannan kisa sinadarin dandano saikisa white papper

  9. 9

    Sannan idan kinga miyar tafara fito da Mai saikisa Mata cray fish bayan mintuna 5 zakiga Mai kwamdan asaman miyar saiki kashe wuta ki sauke ki tuna cewar dole saitayi kauri kuma Mai ya fito kafin ki sauke ta

  10. 10

    Saiki Dora ruwa a tukunya idan ya tafasa ki dauko garin sakwara na leda ki dama da ruwa idan ya damu ki kada kamar yanda zakiyi na semo da ake Masa rude, idan ya dahu mintuna 5 ki tuka kisa ruwa

  11. 11

    Bayan wani Dan lokaci ki sake tukawa ki sauke. Shikenan kin gama

  12. 12

    Kiyi tsarinki yanda kikeso zakuma ki iyayi da normal doya kiyi sakwararki ko kiyi da tuwo ba Dole sai sakwara ba

  13. 13

    Zaki iya cin miyarnan da duk abunda kijeso, Danni washe gari da safe ma yarana sunci miyar da 🍞 bread 😂😂

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Meenat Kitchen
Meenat Kitchen @meenat2325
rannar
Kano State
my name is Amina Mohd Sani, cooking is my fev,cooking is my hubby......
Kara karantawa

Similar Recipes