Tuwan samo da miyar alaiyahu

@Rahma Barde
@Rahma Barde @cook_15125852
Katsina

Wanan girki yana da dadi kuma yana kara lfy ku gwada ku gani

Tuwan samo da miyar alaiyahu

sharhuna da aka bayar 2

Wanan girki yana da dadi kuma yana kara lfy ku gwada ku gani

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Semo rabin leda
  2. 8Tumatur
  3. 3Tattasai
  4. 2Attarugu
  5. 2Albasa
  6. 1/4Manja kofi
  7. D'and'ano
  8. Tafarnuwa2
  9. 1Citta
  10. Nama rabin kilo

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki daura ruwa a tukunya idan ya fara tausa ki dama garin samo din kiyi talge da shi bayan nan sai ki rufe ki bashi minti 10 ya taso ya dahu sai ki tuka da sauran garin da ya rage har yayi iya kaurin da kike so sai ki yayyafa ruwa ki rufe minti biyar yayi

  2. 2

    Sai ki dawo gurin miyar ki ki gyara kayan miyar ki ki markada su sai ki daura mai akan tukunya ki yanka albasa idan ta fara kamshi sai ki zuba kayan miyar ki ki zuba d'and'ano da kayan kamshi ki rufe ki koma akan naman ki zaki wanke naman ki da ruwa mai kyau sai ki yanka albasa ki zuba kayan kamshi ki daura akan wuta ki rufe

  3. 3

    Sai ki yanka alaiyahun ki ki wanke sa tas da dan gishiri ki zuba ga abun tace shinkafa ki tsane sa sai ki zuba Shi cikin kayan miyar da kike soyawa ki motsa ki zuba naman ki ki motsa shi ki rufe minti ukku tayi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
@Rahma Barde
@Rahma Barde @cook_15125852
rannar
Katsina

Similar Recipes