Samosa

Masu dafa abinci 10 suna shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Filawa kofi biyu
  2. Gishiri rabin cokalin shayi
  3. Nikakken nama
  4. Kayan kamshi
  5. Albasa rabi
  6. Mai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki kwa6a filawa da gishiri da ruwa ya yi tauri. Sai ki buga shi sosai. Ki gutsura girma girman da kike so. Ki baza ya yi fadi ki fitar da shi da abu zagayayye. Sai ki barbada fikawa ki dora daya kan daya. Ki dora a kaskon da baya kamu. Sai ki saka wuta kadan a hankali gaba ya gasu sai ki juya wancan sashen. Idan kin gama duk sai ki sauke ki rarraba.

  2. 2

    Ki dafa nikakken naman da albasa da kayan kamshi. Idan ya yi sai ki sauke.

  3. 3

    Ki yanka waccan filawar gasassa sai ki yanka biyu. Ki zuba naman a ciki sannan ki ninka shi ki shafa damammiyar filawa zakiga ya manne. Ki fitar da shi kusurwa uku.

  4. 4

    Ki soya a cikin mai

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
rannar
Kaduna
I absolutely love cooking. I can merrily state that my kitchen is my playground in every sense! My mother has always been a wonderful cook, and I feel she is my inspiration.
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes