Dambun shinkafa(a gargajiyance)

Firdausy Salees
Firdausy Salees @cook_12401542
Kano

Kakata gwanace gurin girka abinci irin na gargajiya (itace sirrin iya girkin gargajiyata🤣 )a duk sanda zanyi dambu nakan tuna da yadda takeyin nata da madambacci ta manne bakin da kuka😂🤣

Dambun shinkafa(a gargajiyance)

Kakata gwanace gurin girka abinci irin na gargajiya (itace sirrin iya girkin gargajiyata🤣 )a duk sanda zanyi dambu nakan tuna da yadda takeyin nata da madambacci ta manne bakin da kuka😂🤣

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Saa biyu(2hours
7 yawan abinchi
  1. Barjajjiyar shinkafa kofi uku (3cups)
  2. Gyada kofi daya(1cup)
  3. Zogale (danye)
  4. Attaruhu,tafarnuwa da citta danya
  5. Albasa(sliced)
  6. Seasoning powder(sinadarin dandano)
  7. Kayan kamshi(spices)
  8. 2/3 cupmankuli(veg oil)
  9. for the sauce
  10. Diced chicken breast
  11. 1big onion (sliced)
  12. 2scotch bonnet (grounded)
  13. Minced ginger and garlic
  14. Curry,thyme & spices
  15. 1 tspdark soy sauce
  16. 2 tspveg oil/olive oil
  17. 1/3 cupwater
  18. Garnish with sesame seeds(kantu/ridi)

Umarnin dafa abinci

Saa biyu(2hours
  1. 1

    Bayan an kawo miki shinkafarki daga barji saeki wanke tass ki tsane ruwan a colander,saeki juye a buhu kisa a steamer ki rufe sosae yadda turirin bazae dinga fita ba,kiyi steaming dinshi for 1hour or 40mins..

  2. 2

    Ki gyara zogalenki tsaf sannan kisa gishiri kadan ki wanke ki tsane ruwan,ki jajjaga attaruhu,citta danya da tafarnuwa a hade,ki yanka albasa sliced...

  3. 3

    Ki zuba gyada a kasko ki dan soya kadan yadda bawon zaeyi saurin fita,saekisa a turmi ki sassabe sannan ki fece tass,ki zuba oil a kasko ki zuba gyadar ki soya sama sama kisa a side...

  4. 4

    Nan ga abubuwan hada dambunmu kamar hka;

  5. 5

    Bayan ta turarah sae ki juye a roba mae dan girma ki juya sannan ki zuba albasa da hadin attaruhu dinmu..

  6. 6

    Ki juye zogalen kisa seasoning powder da spices,sannan ki juye oil da gyadar..

  7. 7

    Ki juya sosae su hade sannan ki kara juyewa a buhu ki maeda cikin steamer,kiyi steaming dinshi na tsohon(1hour or 40mins)zakiga albasar tayi laushi,zogalen y dahu gyadarmu ta dahu to dambu y kammalah saeci😋💃

  8. 8

    Abubuwan bukata na sauce dinmu;

  9. 9

    Ki zuba diced chicken breast dinki a bowl kisa seasoning powder,spices da dark soy sauce ki juya sosae su hade kisa a side..

  10. 10

    Kisa oil a pan yayi zafi sannan ki zuba sliced onions dinki ki soya sama sama,ki zuba attaruhu,ginger da garlic dinmu da muka jajjaga,saeki soya sama sama ki juye a bowl kisa a side,kisa oil kadan a pan din ki zuba spicy diced chicken breast kita juyawa har ya dan soya...

  11. 11

    Saeki juye albasarki akae ki juya,ki zuba ruwa kadan hka,sannan ki kara maggi,curry da thyme ki juya,ki rufe for 3mins ruwan y zamana saura kadan toh shikenan kin gama

  12. 12

    Saeki serving ki barbada kantu/ridi a saman sauce din and enjoy🤩😋😋

  13. 13

    Anaci ana korawa da lemo mae sanyi🤣🤣

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Firdausy Salees
Firdausy Salees @cook_12401542
rannar
Kano

Similar Recipes