Zobo na na musamman

(#zobocontest)A gaskiya zobo abun sha ne mai dadin gaske fiye da sauran abubuwan sha na zamani, ina matuqan son zobo baqi sukan zo gidana musamman don su sha zobo na mai dan Karen dadi da kanshi
Zobo na na musamman
(#zobocontest)A gaskiya zobo abun sha ne mai dadin gaske fiye da sauran abubuwan sha na zamani, ina matuqan son zobo baqi sukan zo gidana musamman don su sha zobo na mai dan Karen dadi da kanshi
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko za ki daura zobo a wuta sai ki wanke bawon abarban ki zuba ki daka citta ki zuba ki zuba kanunfari da ganyen na,a na,a lemun ciyawa (lemon grass) ki bar shi ya tafasa sosai har sai ruwan ya dan ragu sai ki sauqe ki ajiye a gefe
- 2
Ki yayyanka su kankana, goba, da cucumber kowanne ki niqa shi daban daban ki kuma tace su daban Sannan ki ajiye a gefe
- 3
Ki dauko zobon ki ki tace shi ki zuba sugar yadda kike so sai ki jujjuye kayan marmarin nan da kika tace daya bayan daya,
- 4
Ki dauko foster Clark shima ko wanne ki jika shi daban daban kina gauraya Wa kina juye wa a cikin zobon har ki gama idan kin gama sai ki zuba a abu mai tsafta ki saka a cikin fridge yayi sanyi sosai, tagamu sai sha
Cooksnaps
Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!
Similar Recipes
-
-
Zobo na musamman
Zobo na da amfani sosai ajikin Dan adam kuma yana maganin cutittika musamman hawan jini Oum Nihal -
Zobo
#zobocontest daya daga cikin manyan abubuwan sha masu karin lafiya. Kamar yadda muka sani cewa zobo wani ganye ne wanda ake busarwa, a sarrafa shi domin yin abun sha. A irin wanna lokacin na zafi zobo na da matukar tasiri ga al'ummah. Sau da dama nakan yi shi ga iyalina su sha. Princess Amrah -
Abinsha na zobo
Wannan hadin inasansa acikin wannan yanayi na zafi musamman idan yaji kankara #zobocontest Meenat Kitchen -
Zobo na Musamman
Zobo wani nau'ine na abin sha Wanda yake tartare da sinadarai masu kara lafiya a jikin Dan adam. Uwargida gwada sirrin nan ki bamu labari akwai dadi #ZobocontestAsma'u Sulee
-
Zobo
#nazabiinyigirki wannan zobon itake wakiltata akoda yayshe inason shan zobo arayuwata sbd yanasakani farinciki da annushuwa TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) -
Pineapple and hibiscus mocktail
#Team6drink. Kusan kowa yasan amfanin zobo da abarba ta fannin lpy. Wannan recipe din nayi amfani da wasu abubuwa na recipe din mumeena ne, banbancin kadan ne. Dadi kuma baa magana sai wanda ya gwada😋😋😋💝 Zeesag Kitchen -
Zobo
Ina son Zobo saboda amfaninshi ga jikin dan Adam sannan in hadashi ne da kayan lambu da sauran tsirrai don ya bada kamshi mai dadi. Kadan daga cikin amfanin Zobo sune, 1. Yana kunshe da sinadaren Calcium, Iron da fiber wanda suke kara garkuwa ga jikin dan Adam. Sannan akwai acetic acid da tartaric da Vitamin B wanda suke kara lafiya Koda da Zuciya. Sauran abubuwan da nake sawa kuma irin su citta, Kanumfari da cucumber suma duk suna da amfani sosai.#Zobocontest Yar Mama -
-
Zobo
#zobocontextrecipe#Zobo shine juice da nafiso nake yawan yinsa mussaman saboda Mai gidana shi yafi so Maryam Sa'id -
-
Zobo
#zobocontestZobo abin sha neh da ya samo asali tun zamanin da saboda yana da amfani,mahimmanci da inganci a jikin dan Adam.Duk abubuwan da nayi amfani dasu kowanne nada nasa amfanin sosai a jiki.Zobo yana rage kamuwa da cancer,masu hawan jini ciwo sugar suna sha domin shima magani neh sosaiAysharh
-
Zobo da ganyen lemon grass
Zobo da ganyen lemon grass sunada matukar amfani ajikin Dan Adam #zobocontest Meenat Kitchen -
-
Zobo drink
Idan kika gwada wannan zobo me abarba da cucumber,kika barshi yayi sanyi kikasha zakizo ki bani labari😁 asmies Small Chops -
Lemun Zobo
Zobo na da matukar amfani a jikin dan Adam. Shi ya sa INA son hada shi da yayan itace sosai. Hauwa Musa -
Zobo mai kayan hadi
A gaskiya ina son zobo musamma indan yaji kayan kamshi ko yayi sanyi sosai gashi yana kara lfy sosai..#zobocontest.Shamsiya sani
-
Zobo
#Zobocontest Shi dai zobo sanannen abun Sha ne Wanda ake sarrafa shi tun fil azal. Sa'annan ya shahara a wajen magunguna da yakeyi na cutuka daban daban. Ina matukar kaunar lemun zobo musamman idan aka sarrafa shi tare da kayan kamshi irin su citta, kanun fari, masoro, ganyen na'a na'a, da kuma lemun zaki. Wanni hadi na da matukar kayatarwa tare da sanyaya zuciya gami da sa nutsuwa. Phardeeler -
Zobo
#zobocontest Shi dai zobo sanannen abun Sha ne Wanda ake sarrafa shi tun fil azal. Sa'annan ya shahara a wajen magunguna da yakeyi na cutuka daban daban. Ina matukar kaunar lemun zobo musamman idan aka sarrafa shi tare da kayan kamshi irin su citta, kanun fari, masoro, ganyen mint, lemon grass da Kuma abarba. Wanni hadi na da matukar kayatarwa tare da sanyaya zuciya gami da sa nutsuwa. Phardeeler -
Zobo
Zobo dai wani ganye ne Wanda ke fito wa a matsayin furen sure/yakuwa, akwai farin shi akwai ja akwai kuma baki, zobo dai Yana da amfani sosai a jikin Dan Adam musammam in ba'a samishi kayan Zaki ba, Ya na maganin hawan jini sannan Yana wankin ciki da dai sauran su #zobocontest HALIMA MU'AZU aka Ummeetah -
Zobo
#zobocontest lemon zobo na daya daga ckin natural drinks me kara lafiya a jikin dan Adam,musamman ayishi ta fannin komai yazama natural a ciki .shi lemon zobo a yishi ya turu shine yke kara dadi sanan yana kara dadewa a fridge yanakara turuwa da kara dadi sanan kuma yayin da zaki tace zobonki zaki kara maidashi wuta ya tafasa shima yana saka zobo ya kara tsumuwa .lemon zobo na kara lafiya ta hanya daban daban yana dauke da sinadarin masu amfani sosai a jiki. phateemahxarah -
Zobo mai cucumber
Wannan hadin yanada dadi sosai ki gwada zakiji dadinsa #zobocontest Meenat Kitchen -
-
Zobo mai sanyi
Yanzu da zafi ya fara matsowa zobo yana da amfani a jikin mu saan kuma idan mai sanyi ne zaki jika makoshin da shi ina son zobo gaskia @Rahma Barde -
Zobo
Wato wannan zobon da kuke ganin nan nayi shi babu sugar. Muna wani challenge na 7days free sugar challenge. Gaskiya is not easy rayuwa ba sugar. Ina matukar son zaki wadda ya zamana a duk sanda naci abinci sai na samo abu mai zaki ko na sha ko sweet na kwata dashi Ina ganin wannan challenge din I was like shikenan an gama dani dan nasan bazan iya ba Allah da iko kuma sai gashi nayi yau muna day 4 sauran kwana uku ya rageMin na fara shan zaki . Wallahi I can’t wait💃💃😂 Ayshat Adamawa(U. Maduwa) -
Hadaddan Zobo
Wannan hadin Zobo nayi shine ga mahaifita(My MUM)taji dadin shi kma tasa min albarka...zabo shi kanshi magani ne ,Ina masu fama da yawan kumburin ciki indae za a dafa Zobo a Sha cikin yadda Allah mutum zai samu sauki Mama's Kitchen_n_More🍴 -
-
Natural Zobo Drink 🥤
Ina son Zobo sosaiShyasa bana gajia d yi SannanNatural Zobo Yana matukar amfani d Kara lfy a jikin dan AdamBa artificial Zobo ba Mum Aaareef’s Kitchen 👩🍳 -
Fruity Zobo
Abinda yasa yazama na musamman saboda kayan itatuwa da akasa sai yabamu qamshi na musamman, na hadawa baqina sunji dadi. sadywise kitchen -
More Recipes
sharhai