Caramel popcorn

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

mintuna talatin
mutum biyu
  1. Rabin kofi masarar gurguru
  2. 3butter Cokali
  3. Rabin kofi sigari me ruwan kasa(brown sugar)
  4. Cokalin shayi daya na flavour
  5. Kwatan cokalin shayi bakar soda
  6. Narkenken chocolate don ado

Umarnin dafa abinci

mintuna talatin
  1. 1

    Za'a samu tukunya Wanda take rufuwa a dora a wuta tayi zafi sannan a rage wutar

  2. 2

    A saka cokali daya na butter sai masarar gurguru din a juya sannan a rufe

  3. 3

    Idan sunyi zafi za'aji sun fara fashewa sai a dinga jijjiga tukunyar a hankali za'aji yanata fashewa, idan ya gama sai a kashe wutar a juye gurgurun a faranti

  4. 4

    Sai a samo wata tukunyan ko (pan) a zuba cokali biyu na butter a bari ta narke sai a zuba wannan sigari me ruwan kasan a ta juyawa harya narke sannan flavour da bakar soda a juya sosai, a zuba gurgurun a ta juyawa har ko ina ya juyu.

  5. 5

    Idan yayi sanyi sai a sauke Tasha iska sai aci😋😋😋. Idan anaso za'a iya narke chocolate a saka a saman😍😍😋😋

  6. 6

    GARGADI: ba'a cika wuta gurin yin gurguru kuma a dinga jijjiga tukunyar da zarar ya fara fashewa hakan zaisa ko wanne ya fashe

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
maya's_cuisine
maya's_cuisine @cook_14385342
rannar
Nasarawa

sharhai

Similar Recipes