Tuwon qullun gero

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Kwano daya na gero

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zakisamu gero ki gyara sannan ki jiqa ya kwana

  2. 2

    Da safe zaki qara wankeshi sai ki niqa,(niqan ruwa za'ayi)

  3. 3

    Sai ki tace shi,zaki iya amfani da matankadi ko kyallen taci

  4. 4

    Bayan kin tace zaki barshi ya kwanta,amman anfison ya kwana domin tuwon zaifi sulbi

  5. 5

    Zaki sa ruwan zafi kamar yadda kika saba yin tagen tuwon gari amma wannan baya buqatar ruwa dayawa domin anson yayi kauri sosai,saboda haka ko kullun talgen zakiyishi da kauri

  6. 6

    Zaki talgen ya dahu kamar minti 10-15 sannan ki kara wani kullun ki tuqa dai-dai yadda kikeson shi

  7. 7

    Zaki rage wuta ki barshi ya sulala kamar 10-15min sai ki kwashe

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Safiyya Yusuf
Safiyya Yusuf @samgz2703
rannar
Sokoto

sharhai

Similar Recipes