Dafadukar shinkafa da busashen kifi

mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
Kaduna State, Nigeria

Dafadukar shinkafa da busashen kifi

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 2Shinkafa kofi
  2. 2Busashen kifi madaidaita guda
  3. Tumatir,tattasai,tarugu,shambo
  4. Albasa
  5. 1Tomato paste sachet
  6. Dandano
  7. Gishiri
  8. Kayan kanshi
  9. Mai
  10. Hadin citta da tafarnuwa dakakke
  11. Ganyen bay leaf

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko ki gyara kifinki ki cire kayar sai ki wanke ki aje gefe.sai ki yanka kayan miyanki daidai misali ki yanka albasa.

  2. 2

    Ki samu tukunya ki dora a wuta sai ki zuba mai ki sa albasa sai ki rage kadan.idan ya dan soyu sai kisa hadin citta da tafarnuwa nikakke.

  3. 3

    Idan ya dan soyu sai ki sa tumatir dinki na sachet ki barshi ya soyu tsamin ya fita sai ki zuba yankakken kayan miyanki kisa ganyen bay leaf ki soya.kisa dandano,gishiri da kayan kanshi idan ya soyu sai ki tsaida ruwa dai dai yadda zai dafa miki shinkafar.

  4. 4

    Idan ya tafaso sai ki wanke shinkafar ki zuba idan tafara laushi sai ki zuba kifinki da sauran albasa idan yana bukatar karin dandano ko ruwa sai ki kara ki barshi ya karasa dahuwa.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
rannar
Kaduna State, Nigeria

sharhai

Similar Recipes