Dafaffen wake da garin kuli

Ummu HIBBAAN🍝🍓🍉🍇🍌🍜
Ummu HIBBAAN🍝🍓🍉🍇🍌🍜 @fatumar6855
Zaria City, I'm Married💞💞💞

Wannan abincin yana Kara lafiya ,da Karin jini gawanda basu dashi. Sannan ga dadi Ku gwada Ku gani😋😋😋😋

Dafaffen wake da garin kuli

Wannan abincin yana Kara lafiya ,da Karin jini gawanda basu dashi. Sannan ga dadi Ku gwada Ku gani😋😋😋😋

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti talatin
mutumbiyu
  1. Wake gwangwani biyu
  2. Cabbage/latas
  3. Garin kuli gwangwani daya
  4. Tumatir guda uku
  5. Man gyada gwangwani daya
  6. Sinadarin girki guda hudu
  7. Albasa guda daya

Umarnin dafa abinci

minti talatin
  1. 1

    Uwar gida zaki wanke wakenki ki daura a wuta, kisa albasa da magginki guda biyu,ki barshi ya dahu sosai yayi lubus.

  2. 2

    Sai ki dauko cabbage ko latas kiyayyanka kisa gishiri ki wanke sai ki tsane, sai tumatir ki yayyanka, sai ki zuba a basket ya tsane.

  3. 3

    Sai kisa garin kulinki a turmi kisa Maggi guda biyu ki daka ya hade da kulin.

  4. 4

    Ki daura manki a kan wuta ki soyashi.

  5. 5

    Sai a samo plate a zuba wake asa cabbage ko latas asa tumatir a gefe a zuba garin kuli asa mai, 😋😋😋😋 aci dadi lafiya

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ummu HIBBAAN🍝🍓🍉🍇🍌🍜
rannar
Zaria City, I'm Married💞💞💞
kullum inason koyan abin da ban iya ba, kuma ina son gwadawa🍕🍤🍗🍜🍡🍝
Kara karantawa

Similar Recipes